Mace mai hankali da ruwan sanyi take dafa Ganda!Ku Yi Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana πŸ””πŸ””πŸ””

Mace mai hankali da ruwan sanyi take dafa Ganda!

Ku Yi Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana πŸ””πŸ””πŸ””

Ta ga saΖ™wannin SOYAYYA kala-kala a wayar mijinta. Ta Ι—auki lambar ta rubuta: " Nagode sosai baiwar Allah, Allah ya saka miki da alheri.
Tun da mijina ya kwanta rashin lafiya, Likita ya tabbatar Ciwon HANTA ke damunsa, shi ke nan ya daina dariya. Abin ya Ζ™ara muni shekara 4 baya, lokacin da likita ya tabbatar da cewa yana da taΙ“in hankali.

Shekara 5 banga mijina yana jin daΙ—i da murna da walwala ba sai da ya haΙ—u da ke. Nagode sosai, ina Ζ™aunarki da gaske, Allah ya kawo ki mu yi zaman lafiya....!!

Tun daga ranar  wayarta ta daina shiga, in ya je gidansu ta daina fitowa, in ya tura saΖ™on kar ta kwana ta daina ba shi amsa. Daga Ζ™arshe ta dannawa lambarsa "Block"

Post a Comment

Previous Post Next Post