SHIN SANYA YATSA A GABAN MACE (FINGERING) YANA DA ILLAHTAMBAYA?

SHIN SANYA YATSA A GABAN MACE (FINGERING) YANA DA ILLAH

TAMBAYA?
Aslm malam naga kuna ta magana akan sanya hannu a gaban mace akwai matsala to ni kuma gaskiya matata na riga na saba mata da sanya hannu amman ba can ciki ba, dan kan nan dai shi nake mata wasa da shi a haka na saba mata nake gamsar da ita sannan in yi nima saboda duk abinda za muyi.

Idan na fara to da wuri nake releasing 5 to 10 minutes har na yi releasing to ita kuma a hakan bata yi to da na lura sai in cigaba da yi mata da yatsa har ta yi ko kuma kafin in fara ma sai na yi mata na tabbatar ta gamsu sannan. To yanzu malam me ya kamata inyi naga kace akwai matsala sanya hannu a gaban mace.

AMSA!

Lallai gaskiya ne sanya hannu, watau dan-yatsa, a cikin gaban mace (fingering) domin motsa mata sha'awa yana iya haddasa mata hatsarin kamuwa da kwayoyin cuta. Dalilin fadin haka shine saboda hannu yana dauke da dumbin kwayoyin cuta iri-iri wadanda idanu basu iya ganinsu. Kuma shine dalilin da yasa yawan wanke hannuwa yake ɗaya daga cikin hanyoyin rage kamuwa da cututtuka.

Idan da ma'aurata zasu rika yin fingering da kulawa, to, da hatsarin kamuwa da cututtukan zai ragu. Kulawar anan ita ce a tabbatar da tsabtar hannu ta hanyar wanke shi sosai a lokacin da za'a yi, da kuma tabbatar da an yanke kumba.

Amma shawara anan ita ce kayi kokarin canzawa daga yi mata fingering ɗin zuwa yin wasanni da wasu sassan jikinta na daban a lokacin da zakuyi Sunnah. Hakan yafi kwanciyar hankali.

WALLAHU A'ALAM

Post a Comment

Previous Post Next Post