Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki:1. Iya Taku

Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki:

1. Iya Taku

Takunki a lokacin da kike gabansa da tsayuwarki da zamanki, dole ne ya zamo na musamman.Ya kasance daban kuma cikin salo na ɗaukar hankali. kar ki kasance mara kuzari ko kina nuƙu-nuƙu a yayin da kike tare da shi.

2. Ku yi Siyayya Tare

Yana da kyau kuna yin siyayya tare musamman ƙananun kaya masu ɗaukar hankali, wanda za ki yi masa kwalliya da shi, shi kaɗai. Kuma ki nemi zaɓinsa a kan irin wanda yake so, hakan zai saka shi ya kasance cikin zumuɗi.

3. Ado Da Kwalliya

Ba dole ba ne, sai kin caɓa kwalliya mai yawa sosai ba, a wasu lokutan canza yanayin gyaran gashinki ko gyaran fata yana jan hankalin mai gida. Ko Kuma canza launin jambaki ko ƙara wani sabon launi a kan fuskarki wanda bai saɓa gani ba.


Post a Comment

Previous Post Next Post