Lafiya Uwar Jiki: Abubuwan Da Rashin Shan Isasshen Ruwa Ke Haifar Wa

Lafiya Uwar Jiki: Abubuwan Da Rashin Shan Isasshen Ruwa Ke Haifar Wa:

🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛🥛
Masu iya magana kan ce, ruwa shi ne rayuwa, amma mafi yawan mutane ba su faidantuwa da alfanun da ke tattare da shan isasshen ruwa wanda hakan kuma yana haifar da wasu illoli a jikin dan Adam ta yadda su kansu ba su ankara ba.

Ga wasu daga cikin illolin rashin shan isasshen ruwa:

🔮 Ciwon Kai; rashin shan isasshen ruwa yakan haifar da ciwon kai mara nauyi wanda kuma shan mara sanyi na kawo karshen irin wannan matsalar.

🔮 Bushewar. Baki; duk mutumin da ke fuskantar Bushewar baki akai akai, to tabbas ba ya shan isasshen ruwa.

🔮 Rashin shan isasshen ruwa yakan janyo raguwar yin fitsarin tare da canja launin fitsarin, wanda hakan wata alama ce da ke nuni cewa akwai bukatar mutum ya nemi ruwan sha isasshe.

🔮 Rashin shan isasshen ruwa yakan haifar da gajeruwar yunwa musamman bayan cin abinci ba da jimawa ba, don haka a irin wannan yanayi, mutum ya sha ruwa kafin ya ci wani abin kwalama.

🔮 Haka ma, rashin shan isasshen ruwa yakan haifar da jiri.
🔮 Rashin shan isasshen ruwa yakan haifar da bushewar fatan jiki.
🔮 Rashin shan isasshen ruwa yakan haifar da matsalolin ciki
🔮 Rashin shan isasshen ruwa yakan haifar da bushewar ido.

Post a Comment

Previous Post Next Post