YADDA AKE HADA HALAWA DA KUMA YADDA AKE SHAFATA A CIKIN JI
YANDA AKE HADA HALAWA, DA YADDA AKE SHAFA TA A JIKI
Yadda ake hada halawa don gyaran jiki.
• Sugar
• Ruwa
• Lemon tsami
Zaki daura ruwa a kan wuta kadan kamar quarter na cup/gongoni in yayi zafi sai ki kawo sugar kamar 1 cup/gongoni ki zuba sai ki kawo lemon tsami mai ruwa guda 1 ki matse akai, kar ki sa wuta da yawa, sai kiyi ta juyawa a hankali har ya zama golden brown amma kar ki bari ya daskare.
Zai yi kauri amma zai dinga debuwa misali in kin diba ba spoon kika daga zai dinga malala haka, I hope de kun gane, to shikenan sai a kashe wuta in ya dan huce sai a samu container a zuba. Kuma zaki iya tun farko ki hada ruwan da sugar din da lemon tsamin duk lokaci daya ki dafa
Yadda ake anfani da halawa don gyaran jiki.
Shi halawa dama mainly dan cire gashin jiki akeyi da kuma dead skin. In babu gashin zakiji jikin yayi smooth sosai sai kuma dead skin din da yake cirewa zai sa fatan yayi haske da laushi.
To in short ko ina a jikin mutum ana iya yin halawa sai dai ko fuska.
Da farko zaki debo halawan da kan yatsun ki biyar, in kika zo shafawan sai kisa yatsu hudu banda babban yatsan wato yatsu hudu zakiyi amfani dashi wajen shafawan, kar ki shimfida yatsun kuma, sai ki shafo daga sama zuwa qasa misali in qafa zaa fara daga guiwa zuwa idon sawu zaa raba tsayin qafan gida uku ko hudu.
To sai ki shafa daga sama zuwa qasa to kar ki dauke yatsun sai ki kuma yin baya dashi ki cire da yatsu biyar da sauri. Haka zakiyi tayi in kika yi gaba kika shafa sai kiyi baya ki cire, haka zakiyi tayi har kiyi ko ina.
Kadan zaki dinga debo halawan kina shafawa in kika ga yayi datti, to sai ki kuma debo sabo ki ci gaba har ki gama.
Wasu zaki ga sun labto halawan sun yaba a jiki sun manna sosai sannan sai a ja a fizge to hakan ba daidai bane.
Idan halawan ya rage zaki iya ajiye shi, ko da yayi tauri duk ranar da kika tashi anfani sai ki dumama in kuma a container yake zaki iya sashi a ruwan zafi.