AMFANIN GANYEN NA'A NA'A GA LAFIYAR MU.
SHARE.....✎
Bincike ya nuna cewa, shukar na’a-na’a wadda ta fito daga dangin ciyayi ake kira mentha ta samo asali ne ta hanyar auren-shuka, Hybridization a Turance, wato auren shuka mai suna ‘watermint’ da kuma wata shukar mai suna ‘spearmint’.
Ana kuma samun man na’a-na’a da ruwanta a kasuwanni domin alfanu daban-daban. Bincike ya nuna cewa na’a-na’a na da amfani da yawa ga lafiyar dan’adam. Ana sarrafa ta hanyoyim daban-daban domin cin moriyarta
Ga wasu daga cikin alfanin na'a-na'a ga rayuwar dan Adam:
1. Tana magance matsalar ciwon ciki da rashin fitar bahaya cikin sauki. Ana hada shayin na’a-na’a ko a zuba manta cikin shayi marar madara sai a sha.
. Tana saukaka narkewar abinci. Ta kan taimaka wajen narkar da abinci yadda sassan jiki za su yi amfani da shi.
3. Tana maganin dukkanin wata dangin cuta ta sanyi ko mura. Ana amfani da man na’a-na’a ko ganyen a tafasa cikin shayi marar madara, haka kuma, za a iya amfani da man na’a-na’a cikin ruwan zafi, a yi turiri, a lullube da mayafi wato sirace a Hausance.
4. Maganin ciwon kai. Ana shafa man na'a-na'a a bangaren da kai ke ciwo.
5. Maganin ciwon jiki. Ana shafa manta ga jijiyoyi ko sassan jiki dake ciwo.
6. Maganin ciwon hakori. Ana yi amfani da man na’a-na’a da auduga inda ake diga man ga auduga sa’annan a manna ga hakori da ke ciwo.
7. Ana iya shafa manta a bangaren jiki da ke kaikayi domin samun sauki.
8. Korar sauro. Ana shafa man na’a-na’a a jiki domin kamshinta kadai yana korar sauro.
9. Na'a-na'a ta na kashe tsutsar ciki.
Wallahu a'alamu
LIKE AND SHARE ➡️