BREAST SELF EXAMINATION (YADDA MACE KE DUBA LAFIYAR NONON TA):
MENENE BREAST SELF EXAMINATION?
Breast Self examination: Hanyace da mata ko 'yan mata ke duba ko kula da lafiyar mamansu (Nono) Don gujewa kamuwa da cututtuka kamar ciwon daji na nono ( Breast cancer) dadai sauransu.
Matar dake dauke da wannan cutar babu wani alamun ciwo da zataji tashin farko! Kawai dai wani ɗan tsiro karami ko ƙullutu wanda yake jeji ne (Cancerous cell) zataji cikin Nononta, Wanda akarshe ka iya jawo mata babbar illah da zatasa dole acire nonuwan gaba daya inma anyi sa'a bata warwatsu ba kenan.
Kamuwa da cutar ba laifin mutum bane, ba kuma a kamuwa ta hanyar jima'i, ko yin hulda da mai cutar.
WANE LOKACHI AKEYIN BREAST SELF EXAMINATION?
Duk macen data kai shekara 20 abinda yaisama, anason tadinga yi duk wata musamman kwana 3-5 da fara menses (Al'adarta).
MAFITA SHINE: Duk Macen data kai aƙalla shekaru 20 yana da kyau ta koyi yadda ake duba Nono (breast self exams) domin wannan wata hanya ce da Mace zata iya ita kaɗai a ɗakinta, ko wajen wanka, ko ita da Maigidanta, ta duba Mamanta a madubi ko akwai wani canji ajiki. Gudun kamuwa da wannan ciwo.
ALAMOMIN GANE WANNA CIWO (BREAST CANCER)
Ta yadda da taji wani abu daban kamar:
◾- Jin ƙullutu,
◾- Jin suka cikin nonuwa kamar ana tsira mata allura, ko
◾- Ganin kumburin nono haka nan, ko
◾- Lotsawar wani sashi "dimples a nono, ko
◾- Ganin fitar ruwa-ruwa me jini ko clear alhalin bata shayarwa, ko
◾- Canzawar kalar wani sashin fatar na nono yai kamar jikin lemon ɓawo ko jaja-jajaa
Toh ta garzaya asibiti wajan kwararru !
____________________________________
YADDA AKE YIN BREAST SELF EXAMINATION:
- Mace ta tube agaban ƙaton Madubi 🪞ta ɗora
hannayenta kan kugunta, ta kallesu a natse taga ko akwai wani yanayin canji a fatar ko ƙurji, dimples ko ƙari a jiki, gami da girman su.
- Bayan nan sai ta juya ta gefe ta sake yin haka (wato ta duba gefen dama da hagu) ta ɗaga hannun ta ta kalli har zuwa hammatarta tunda jelar nonon nan ta shiga.
#ibrahilogyhealth