LIKITA BANI DA AURE, AMMA INA DA MATSALAR SAURIN INZALI
________________________________________
Marasa Aure ina son ku sani abinda ya shafi al'amarin jima'i ba'a yanke hukuncinsa bisa zato ko tunani, mutum ya lamince cewa ai kurum akwai matsala saboda kaza...., Ku sani ba'a yiwa sexual health assumption.
Haka siddan baka taɓa experiencing sexual contact ba... Taya za kaiwa kanka hukuncin cewa kana jin kana da matsalar saurin kawowa, ko raunin gaba, ko ƙanƙancewarsa?
Matsaloli irin wannan na sha faɗa cewa; Ko Aure mutum yai yaga yana fuskantarsu bazasu taɓa amsa sunan Matsala bane har sai ya kai watanni shida cif-cif cikinsu batare da ganin canji ba. Matukar likita yasan me yake ba zai taɓa yunkurin bada treatment akan saurin inzali ba ko raunin gaba sai mutum ya shafe watanni shida cif-cif yana fuskantar matsalar batare da ganin wani canji ba.... Ko kuwa in sanda yazo din aqalla yai watanni shida ko shekaru cikinta.
________________________________________
Rubututtuka ne gurɓatattu kullum qara cika yanar gizo suke, wasu na amfani da yunwar mutane gami da fargabarsu suna Daɗa cusa musu tsoro domin samun kuɗinsu ta hanyar tallata magungunansu, wasu kuma na amfani da abubuwan da suke kallowa ko karantowa gurɓatattu a Novels na qarya da gaskiya... suna qara rikita lissafin rikitattu.
________________________________________
Bawan Allah Yadda ka tsammaci lafiyarka wajen jima'i, kuma ka lamincewa ƙwaƙwalwarka to hakan zaka sami kanka tun ma ace dama baka taɓa yi ba. Inbaka sani ba gara ka sani.
Wannan abin daka sanyawa xuciyarka cewar kana da matsalarsa alhalin baka ma da tabbas... shi kaɗai na iya ruguzaka na dun-dun'din, yadda matsalar da kake tunani din zata zo ta tabbata jikinka harta wuce tunaninka... Ta yadda kuma ko likita bazai iya ceto ka ba. Yes! sex baki ɗaya emotion ne, Jiki ke sarrafawa ita kuma kwakwalwa ke aikatawa.
Don haka muddin mutum ya sami matsala a tunaninsa game da kansa toh ba maganin karfin maza ba ko rodi za'a dasa a gabansa babu abinda zai iya tsinanawa. Mummunan tunani ga abinda ya shafi jima'i na tasiri a kwakwalwa har ya taba lafiyar mutum ta fannin.
________________________________________
Wannan kuma shine abinda ke faruwa hatta ga wanda suka riqa aikata mastubartion ko suke kan aikatawa, mutum sai yaje can ya karanto Rubutu mara tushe a bazamo sa yazo ya dame mu..., kan yaji cewa duk wanda yake yin kaza ko ya taɓa yi ya gama samun matsala bazai taɓa iyawa Mace ba....
Toh kuwa muddin ka yadda da hakan, ko kasa shi a ranka har yai tasiri xuciyarka cewa don ka taba masturbation shikenan bazaka iya gamsar da Mace ba, zaka,ke saurin kawowa...To babu makawa ka gama yawo! kuma sai ka sami matsalar saboda ka sawa ranka already.
________________________________________
Wannan ke sanyawa ɗin kusan duk wanda suka riqa yi din abaya ke samun matsala iri guda. In haka kurum ne a duniya kwai wanda yakai fararen fata wannan dabi'ar? Kusan 98% dinsu ba wanda bai aikata ba, Har bayan aure wasu, kuma iyalinsu na gamsuwa dasu still. Basa karya, in kasa Questionnaire ka tambayesu game da masturbation ko kallon videon tsiraici amsoshi zasu baka na gaskiya, har adadin yadda suke a rana zasu faɗama.... Toh Amma duk da hakan kai ka taɓa ganin ko a finafinansu ana musu wani tallan maganin karfin Maza...? Sam A'ah Saboda basu ɗau hakan matsayin wani abu da zai basu matsala ba, shiyasa basu da matsalar.
Wannan ke nuna kana samun matsala a tunani shikenan ka gama yawo a komi ma ba sai jima'i. Don haka in abaya ka zamo me masturbation to ka dauka ya wuce, in har yanzu kana yi kai kokarin bari, ka tuba ka daina tunda addinin mu Malamai masu rinjaye sun tafi akan babu kyau. Sannan ka sanyawa ranka ko ranki cewa ƙalau kake baka da matsalar komi. Sai ka zauna lfy.
Shi masturbation da zina release dinsu ba ɗaya bane da aini shin in ace da iyalinka kake, duk su cikin fargaba da tsoron karma wani yazo ya ganka ko kuwa ai sauri a fice ake... Don haka bazaka iya yanke hukuncin lafiyar ka ta nan ba.
Sannan dangane da kankantar gaba nasha faɗa mude a likitance bamu da wani maganin qara girman azzakari... Haka ma a gargajiyancen babu, duk wanda yace wai yana dashi zai baka toh damfara ce, wannan shine batu na gaskiya.
Aci me kyau, asha me kyau kurum
✍🏻
Ibrahim Y. Yusuf
________________________________________