kamshin jiki

*KAMSHIN JIKI*
♦ Da farko a zuba lalle a tukunya a sa ruwa, a dora a wuta ya dahu sosai, sai a sauke, a tace, sannan a cire garin lalle gefe sai a mayar da ruwan kan wuta, a rage wuta sai a kawo madarar turare na sandal bakhur, damarar Ledus da madara Musk, sannan a bari ya tafasa sosai, sannan a sauke, in ya huce ki nemi jarka ko galan mai cin lita hudu ki juye a ciki, duk sanda ki ka yi wanka, in kin gama sai ki kawo wannan hadin ki zuba kadan a bokiti, sai ki kara ruwa kadan sai ki dauraye jikinki da shi, kar ki goge jiki ki bar shi ya bushe, za ki sha mamakin yadda kamshin zai zauna a jikinki.
♦ Sannan kuma ku zamto masu yawan mu’amalla da turare a koda yaushe, in har kun san baku da hanyar wadannan to ku zama masu yawan sa turaruka a wurare shida kullum a jikin ku.
Bayan kunnenku
Dantse
Sharaba
 Wuya
kasan nono da sauransu.
♦ Gaban ku kuma ku dan samu auduga ku jikata da madarar misk (Aisha) sai a dinga matsi dashi, haka zaisa shima gabanki (farji) ya dinga diban kamshi duk lokacin da maigida yakai ga wurin.
Macen da take so ta riqa yin qamshi mai xaukar hankali sai ta nemi:
Kafi amarya qamshi
Garin ambar.
Garin miski.
Garin kaninfari.
Kafun-kafun.
Sai ta cakuxasu a cikin baslilin (Vaseline) ta ringa shafawa. Duk inda kika je to gurin zai dinga qamshi ba za'a so ki tashi ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post