yadda ake miyar wake yadda ake yin miyar wake

Yadda ake yin miyar wakeYadda ake yin miyar wake


Abubuwar da za a bukata



1. Wake



2. Man ja



3. Attarugu



4. Busasshen kifi



5. Albasa



6. Gishiri da magi



Hadi



Idan uwargida ta samo wakenta, sai ta jika. Bayan hakan, sai ta cire kowar jikin waken. Sai ta daura ruwa a wuta. Bayan ya tafasa, sai ta zuba waken ya yi ta tafasa har sai ya nuna ya yi lugwi. Sannan sai ta zuba yankakkiyar albasa da dakakken attarugu da manja da busasshen kifi. Sai a jira miyar ta yi ta tafasa na mintuna kadan, sannan sai a zuba magi da gishiri. Hhmmn!! Ana iya cin wannan miyar ne da tuwon shinkafa. Kuma anfi son amfani da ita da rana ko da yamma. Lallai idan maigida ya ci wannan abincin sai kunnensa ya motsa. Da fatan za a girka wa maigida wannan miyar domin armashi da kuma dandano mai gamsarwa!

Post a Comment

Previous Post Next Post