kosai ka uku

*KALOLIN KOSAI🧆🧆🧆 DOMIN RAMADAN IN SHAA ALLAH BY gloden KITCHEN👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣🍜🍲*

*KOSAN SEMOVITA*
Abubuwan buqata👇🏾
Semovita 
Tarugu 
Tattasai
Albasa
Kwai
Maggi da gishiri
Mai

Dafarko kizuba ruwa acikin roba saiki dauko semo dinki kizuba aciki kijuyashi kizuba kayanmiyanki da yankakken Albasa dasu maggi da onga aciki yajuyu sosai saiki fasa kwai aciki kidan Bubbugashi sai soyashi acikin mai.
✍🏾 Gloden 👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣🍜🍲

*YADDA AKE KOSAN ROGO*

Abubuwan buqata👇🏾
Garin rogo 
Atttarugu da albasa
Manja ko Mangyada
Maggi
Dafarko Zaki jajjaga Atttarugu da albasa aturmi
Saiki kawo garin rokonki kizuba akan kayn miyan saiki kawo ruwan zafi kizuba akai karyayi ruwa yadda zaikirbu miki kidaka sosai kikawo Maggi kizuba kikirba sosai zakiga yayi danko saikina gutsira kina marawa
Daidai yadda kikeson girmanshi saiki soya a ruwan mai. Yana da dadi😋
✍🏾 Gloden kitchen👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣👌🏾🍲

*KOSAN ALKAMA*

Abubuwan buqata👇🏾
Alkama ta kanti
Nama
Kwai
Maggi
Attaruhu
Albasa
Mai
Idan kikasamo alkamarki taledace akesaidawa a super market saikijuyeta a turmi kidaka har tayi laushi saiki kwashe a roba saiki jajjaga attaruhu da albasa da maggi da curry da nama wadanda kika tafasa kika daka su saiki juye akan garin alkamar nan kifasa kwai akai kisaka maggi ssaiki kwaba da tauri tauri kidinga dungulawa kinasanyawa acikin mai mezafi kina soyawa kigama kijuye a food flask.
✍🏾 Gloden kitchen👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣🍜🍲

*KOSAN BREAD DA KWAI*

Abubuwan buqata👇🏾
Garin bread
Kwai 
Attarugu
Maggi
Curry
Garin tafarnuwa

A samu busasshen bread a murmushe shi da hannu ya Zama gari (ko kuma a siyo garin bread din a supermarket) a zuba garin bread din a mazubi mai kyau da fadi a fasa kwai kamar guda5 a saka maggi,curry garin tafarnuwa da albasa da aka yanka gutsi-gutsi sai a kwaba kamar yanda ake kwabin kullin sosai ... Sai a Dora mai a wuta da yar albasa kadan idan yayi zafi ayi amfani da cokali gurin dinnan diban kullin ana nasawa a ruwan mai kamar yanda ake yiwa kosan wake,idan ya soyu a kwashe ... Shikenan an kammala sai ci.

Za a iya cin wannan kosan da koko,kunu,custard ko tea domin yin breakfast ko kuma dik lokacin da ake buqata. Gliden kitchen👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣🍜🍲

*KOSAN FULAWA*

 Abubuwan buqata👇🏾
Fulawa gwangwani 2
Attarugu manya 2
Albasa babba 1
Yeast Dan kadan, a iba da yatsa sai 2
Kwai 1
Dunkule 3
Gishiri kadan
Takarnuwa kadan
Kifi (in anaso)

Da farko za a hade fulawar da yeast da dunkule da gishiri a juya sosai. Sai a sa Kwan da sauran kayan hadin ( jajjagaggen attarugu da albasa da tafarnuwa) sai a kwaba da ruwa kamar kaurin kullin kosai.
In an kwana sai a bashi kamar minti 5, sai a Kuma yan yanka albasa asa kifin a juya sannan sai a Dora man a kan wuta. In yayi zafibaai a Rika Iba ana sakawa kamar dai kisai in yayi ja a kwashe. 
Ana iya cin shi haka zalla ko da yaji ko da miyan jajjage.
✍🏾 Gloden kitchen👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣🍜🍲

*KOSAN DANKALI DA NAMA*

Abubuwan buqata👇🏾
Dankali
Nama
Kwai
Attaruhu
Albasa
Maggi
Gishiri
Man gyaďa
Fulawa ko garin busashen buredi

Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu idan yayi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba,sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa yayi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga sai ki ďauko kwai ďanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busashen buredi a ciki ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ďauki farantin suya ki zuba man gyada ki ďora a kan wuta ki dinga ďiba kina zuba wa a cikin man gyada mai zafi idan ya soyu zaki ga yayi brown sai ki kwashe kiyi wa Oga yayi breakfast dashi.
✍🏾Sadeeq's kitchen👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣🍜🍲

*KOSAN DANKALI*

Abubuwan buqata👇🏾
Dankalin turawa 
Nama
Fulawa
Kwai 
Albasa 
Attarugu
Gishiri 
Maggi
Man gyada

Ki jajjaga albasa da attaruhu ki kwashe a kwano ko roba sai ki ďauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi duk ki hada da sauran kayan hadin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyada mai zafi ki soya , akwai daďi sosai.
✍Sadeeq's kitchen👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣🍜🍲

Sadeeq's kitchen🍽️👨🏽‍🍳🧑🏾‍🍳

*KOSAN MASARA(CORN AKARA)🧆🧆🧆*
Mutanen Edo state suna kiransa da EKOKA

Abubuwan buqata👇🏾
👉🏾Busasshiyar masara(ja ko farar masara dik wacce aka samu)
👉🏾Albasa
👉🏾Attarugu
👉🏾Gishiri
👉🏾Manja
👉🏾Kwakwa

Za a wanke masarar sai a tafasa ta Na 40-1h(mintuna40 zuwa awa daya) bayan nan a tace a wanke a zuba a blender tare da albasa da attarugu(za a iya zuba gishiri tin a nan) sai ayi blending (ba tare da an saka ruwa ba,ba a buqatan a saka masa ruwa kuma ba a buqatan nikan yayi laushi sosai) bayan an nika zai futo kaman za a yi kosan rogo ,sai a mulmula shi ta kowanne shape da ake buqata a soya da manja(normally anfi suyansa da manja amma idan ba a buqatan hakan sai ayi da Wanda ake so) kamar yanda acikin video nashi za a gan anyi amfani da both manja da kuma mangyada yayin suyansa. Amfanin kwakwa anan shine ana cin kosan yayin da ake gutsiran kwakwa ne(kamar yanda ake cin kwakwa da dabino) yin hakan yana da dadi sosai,sai Wanda ya gwada zai Sani. Shikenan an kammala Kosan masara🧆 sai kuma ci😋😊.
✍🏾Sadeeq's kitchen👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍛🍝🥣🍜🍲

*KOSAN WAKE*

Abubuwan buqata👇🏾
Surfaffen Wake
Attarugu
Tattasai
Albasa
Gishiri
Maggi fari
Maggi

Zaki wanke surfaffen waken ki tas ki hada da attarugu,tattasai,albasa ki markado yayi laushi Sai ki zuba gishiri,maggi,da farin Maggi ki buga shi sosai da sosai (saboda KOSAI yana buqatan bugu sosai). Sai a soya a ruwan mai mai zafi. Idan yayi golden brown a juya dayan gefen,idan sun soyu a kwashe. Hakan za a rika Yi har Sai an kammala. Kuma ana tuyar ana kara buqashi.
Note:-
KOSAI ba ya buqatan wani hayaniyar kayan hadi,yafi dadi idan ba a Yi masa hadi mai yawa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post