macaroni and beans

MACARONI AND BEANS JALLOP,KUNUN GYADA,FLOUR BALLS AND WATERMELON JUICE

*JALLOP DIN MACARONI DA WAKE*
Abubuwan buqata👇🏾

Wake
Macaroni
Albasa tare da lawashin ta
Mai
Attarugu
Tattasai
Maggi (Sinadarin dandano)
Curry
Gishiri

Da farko zaki tsince wakenki ki a wanke sai a dafa shi (yayi dahuwa kamar 3/4) sai a tsane shi a kwando. A gefe daya a zuba Mai da yar albasa (kada a bari tayi ja) sai a zuba jajjagen attarugu da tattasai a soya sai ki tsayar da ruwan sanwarki. Sai a saka Maggi,gishiri,curry, a rife idan yatafasa sai a zuba macaroni idan ta kusa dahuwa sai a zuba waken tare da yankakken lawashin albasar ki,ki rife su karasa dahuwa shikenan an kammala.
✍🏾Sadeeq's kitchen

*KUNUN GYADA*

Abubuwan buqata👇🏾
Gyada
Farar shinkafa
Sugar
Madara (idan da Hali)
Lemon tsami (ko ruwan Dan tsami)

Da farko zaki soya gyadar ki sama-sama ki murjeta ki cashe (dik ki fitarda bawonta tas (ta kasance fara tas) sai ki hada da farar shinkafa ki jika su kafin a markada a tace sai a zuba a tukunya a dora kan wuta,ana dorewa za a fara juyashi da muciya saboda kada ya kama a kasan tukunyar, hakan za a yita juyashi har sai ya Yi kauri sai a matse ruwan lemon tsami ko ruwan tsami (amfanin saka ruwan tsami ko hakan tana taimaka wa kunun rashin tsinkewa ko da kuwa ya kwana ne kuma ba zaiyi tsami ba) Idan kaurinsa ya maki yanda kike so sai ki sauke daga kan wuta a zuba sugar da madara (idan akwai wadatar madarar,idan ma Babu ba matsala bane za a iya sha a hakan) sai sha😋😋😋
Amfanin soya gyadar,hakan zai sanya kamshin gyadar futowa sosai ,Wanda hakan zai shanya a shanye babban kofi1 mutum bai sani ba.
✍🏾Sadeeq's kitchen

*FLOUR BALLS*🧆🧆

Abubuwan buqata👇🏾 
Flour 2cups
Kifin gwangwani1
Albasa
Attarugu 
Yeast karamin cokali 1
Man gyada
Kayan kanshi
Gishiri 
Maggi 

 
Za a fara da zuba yeast cikin ruwan dumi, sannan a hankali za a rika zuba filawa ana juyawa, sai a rufe a sa a rana kamar 3-4hrs. Bayan wann

Post a Comment

Previous Post Next Post