kwai cikin doya

Masha Allah**

Ga alkawari nacika
**Kwai cikin doya**

Kayan haɗi
Doya
Mai
Tarugua
Albasa
Ginger and garlic powder
Black pepper
Kwai
Garin bredi
Maggi
Gishiri

Procedure
Kidafa doyarki da gishiri da ɗan sukari kudakata kamar dai zakiyi sakwara ki aje gefe
Kidafa kwai kiɓare ki aje gefe
Kisaka mai kadan a fry fan kisa albasa seki zuba nikakken namanki kisa tarugu kadan dasauran kayan kamshi dana lissafa ☝️ kisa kayan ɗanɗano da ɗan gishiri kibarshi yadan sulala (karki sa ruwa idanma kinsa karki cika) seki dauko dakakkar doyarki ki mulmula kitaba seki saka naman nan ki aza ƙwai sama seki mulmule kamar ball idan kingama seki kada kwai kisa Black pepper sbd kanni kidinga tsoma balls din cikin kwai kisa cikin garin bredi kisoya cikin mai 😋 har yayi golden brown shikenan kingama 😋

Note;
Kiyi 'yar souce sekici da ita zaki iya jollop ma'ana zaki iyasa kayan haɗinki cikin doyar base kinyi miya ba
Idan bakida nama just kisaka kwanki ya wadatar
Kuyi hakuri da gakeran jawabi 🥰

Musha ruwa lpy ❤️❤️

Post a Comment

Previous Post Next Post