Madara ruwa ta waken suya

Yadda ake madarar ruwa ta waken suya 

Waken suya 2cup 
Kwakwa babba guda 
Dabino
Sugar idan kina bukata 

Zaki jika waken suya ya dauki kamar awa daya ki surfa ki fudda dusar jikinn koh ki nika shi sama sama ba nika sosai ba yadda bawon waken zai fita sai ki markade shi ki tace da abin tata koko kina iya kara ruwa idan yayi kauri sosai yadda madara zata fita sosai sai ki aza akan wuta 

Gefe guda ki markade dabino idan mai laushine idan mai tauri ne ki cire kwallon cikin ki jika ki markade kwakwa ki. tace ki ajiye gefe shikenan

Ki koma ki dubin waken ki idan ya dauki 40min ko 50min zuwa awa guda zaki ga kamar yana a sama ya dena gafi ya kama kamshi sai ki xuba dabino ki sauke sai ki xuba kwakwa ki ki juya ki kara tacewa kisa sugar kina iya sa flavour sai kisa a fridge shinkenan

Post a Comment

Previous Post Next Post