man karas

**Masha Allah**
**Man karas 🥕🥕

Kayan haɗi**
Man zaitun
Karas

Yadda akeyi

1️⃣Zaki gurza karas ɗinki seki daura fry fan ɗinki kisa man zaitun seki soya karas ɗinki dawannan man idan yasoyu seki tace idan kuma kunbari yakone ke kika sani 🤣 shikenan kingama

2️⃣Zaki gurza karas ɗinki seki shanyashi cikin rana idan kuma kinada irin abunnan na en gayu yama sunanshi 🤔 yawwa rehydrator oho kudai kuka sani 🙄 so de ake yabushe ƙarau idan yabushe seki dauko kwalba kizuba shi seki zuba man zaitun ciki har yahau kan karas ɗin seku rufe sosai kije ki aje kullum kidinga ɗaukoshi kina girgiza wa har na tsawon kwana 6_7 se ki tace shikenan kingama

3️⃣Ki gurza karas ɗinki seki dauko kwalba irin ta bama kizubashi seku dauko man zaitun kizuba kitabbatar yahau kanshi seki rufe sosai kibarshi yakwana ya wuni seki tace kimaidashi a kwalba kirufe kibashi awa 4_5 zakiga ruwan karas ɗinki yakwanta to seki tsiyaye man kifitar da ruwan sbd ba'a bukatar ruwa aciki sbd lalacewa shikenan kingama seki zuba a kwalba

Note;
Kidaure kiyi man karas ɗin nan dakanki sbd majority wanda ake saidawa bashi bane

Hanyoyin sarrafa man karas 🥕

Ana soya kwai dashi
Ana fancake dashi
Ana kitso dashi
Ana shafashi a jiki

Kaɗan daga amfaninsa

Yana maintaining fata daga saurin tsufa kinada shekara 60 amuki kallon 40 
Yana gyara fata sosai
Yanasa santsin gashi da taushi yanadai gyara kai sosai

Nagaji me shago bani multina guda daya da madara zanbaka idan nadawo daga dubai 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️
Cornflakes natafe in sha Allah

Se mun haɗe 💃💃😘

Post a Comment

Previous Post Next Post