farfesun ganda

**FARFESUN GANDA**

Birni naje senaga ganda nace asiyo man ta ɗari aka siyo man ita bata wuce yanka huɗuba nalamushe naji kamar nashahi mota 🙄, aikuwa abinnan yabani haushi,inadawowa gida ko daka banshigaba nawuce store naɗauko busassar gandata tun ta karamar Sallah tsabar kyuwa tahanani ingyarata, najikata takwana
Washegari nadaukota nasa soson waya da klin namata wankin babban bargo 🙅,sena daurata awuta takara tafasa nasauke nasata cikin ruwan sanyi nakara saka soso nagurjeta tayi gwanin kyau,sena yayyankata

Kayan haɗi
Tarugu
Tattasai
Albasa
Citta
Tafarnauwa
Masoro
Ɗaɗɗoya
Lawashin albasa
Daddawa
Maggi
Mai
Gyadar miya

Procedure;
Zaki daura tukunya kisa albasa da ɗaɗɗoya koda ganye 3 ce idan kuma bakida ita ke kika sani 🤣, sekisa jajjagaggen tarugunki da tattasai, kijujjuya,seki dauko gandarki kisa dama kindaka citta da kanumfari da tafarnauwa da masoro da gyaɗar kamshi da lawashin albasa busasshe,da dadawa seki saka kisaka ruwa kirufe kibarta ta ɓararraka sosai,idan takusa seki saka maggi da gishiri da ɗaɗɗoya ganye 2 ko daya kibarta ta dahu sosai idan ma baki bari tadahuba ke kika sani haƙorankine ba nawaba 🤷,

Note;
Dahuwar ganda bisa gas tana daɗewa bata ɓararraka ba hakan kuma yana haifar da bannar gass
Idan kinada electric to kiyi amfani dashi idan kuma bakida shi kiyi da gawayi
Idan kinada pressure pot to kiyi amfani da ita zata dahu nan danan
Idan kuma baki da ita kijefa cokali 2 cikin sanwarki
Wannan yafi Kowane mahimmanci
Yanzu nacinye tawa idan kindafa taki kitabbatar kin ijeye mani rabona nima mantawa nayi na ajemaki yasin 🙄

Idan kinyi daidai ☑️ zakiga daidai ☑️
Idan bakiyi dai daiba ❎ ke kika sani 🤣🤣

Ammafa gandar tahaɗu 😋😋

Se mun haɗe 💃💃😘

Post a Comment

Previous Post Next Post