Kiskuren dasuke Bata Girki gishiri

*KUSKUREN DASUKE BATA GIRKI*

*GISHIRI*
idan kinsan girkinki ke kadai ce kobeda yawa kiguji yawan amfani da gishiri domin kuwa muddin kina saka wadataccen maggi to gishiri zedinga miki yawa

*FRIDGE*
duk abinda kikasan zaki barshi ya kwana kiguji saka mishi kwai ko kuma madara musamman idan ba fridge zakisa ba

*KIFI*
kilura gurin sarrafa kifi beson jagwalgwale hannu yana saurin bata kifi kidinga kulawa

*KANWA*
idan kanwarki bata da kyau kobaki da isasshiya kokuma baki da ita to karkiyi danwake domin kuwa bazae taba yin dandanoba hakanan kada kice zaki yawaita shi

*SPAGHETTI*
sphagetti batason spices dayawa hakanan bata son adafa ta da tafassahen nama ko ruwan nama dandanonta beyin dadi sedae kisoya nama kijefa aciki ko kuma kisaka mata kifi hakanan koda wasa karkisakawa sphagetti kitse

*CHIPS*
kilula idan zaki soya chips gishiri kawae ya wadatar karkice zaki saka maggi hakan ba gata bane taste din bekai na gishirin dadi

*MASA*
Idan xaki waina wato masa ki kula sosai albasa tana kara dadi amma idan tayiwa waina yawa tana bata taste din karkice zaki kwaba ta da albasa koki markada yana sakawa albasar tajima tana bugan kullin har taste din ya chanja.

*DADDAWA*
Ita daddawa tana qarawa abu armashi ba ayin farfesu babu daddawa ki kula koda na kifi ne daddawa itace sirrin farfesu hakanan cikawa farfesu Mai ko manja nasa taste din yakoma wani abu daban

*BLACK TEA*
kikula wajen dafa black tea bakowanne irin ganyayyaki ake sakawa ba anfison ganyen yazamanto kala guda sauran kuma kayan kamshine idan bahaka ba zeyi daci ko bauri

*PEPPER MEAT*
kikula gurin yin peper meat ko chicken dole sekin dan soya sannan kisake hadeshi idan bahaka ba zeyi karni

*TAFARNUWA*
 Ita tafarnuwa anfiso asoyata ne afarkon girki nanne taste din yake dadi amma karkice zaki zubata akarshen girki zaki gagara ci musamman miyar kadi hakanan ba asaka tafarnuwa a alale ko dambu da makamantansu

Post a Comment

Previous Post Next Post