yadda ake girka kazar indiyawa

YADDA AKE GIRKA KAZAR INDIYAWA

Assalamu Alaikum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. Kamar yadda na saba fada muku, yana da kyau idan za a yi girki a rika taba birni da kauye har da kasashen waje. Hakan ya sa a yau na dauko muku irin girkin mutanen Indiyawa ‘chicken curry’. Tare da fatan za a gwada shi wata rana ga mai gida ko kuma ga manyan gobe domin kara ilimantar da su a kan abincin kasashe waje.

Abubuwan da za a bukata
· Man zaitun
· Albasa
· Kori
· Madara (nonon da aka tafasa)
· Gishiri
· Dakaken masoro
· Heaby cream (za a iya samu a manyan shagunan da ke sayar da kayan girke girke)
· Kaza daya
· Timatir guda daya.
· Ganyen kori.

Hadi

A wanke kaza sannan a silala ta da kayan kamshi da albasa da magi har sai ta yi laushi sosai. Sannan a sauke ta huce. A sami wuka a daddatsata kanana sannan a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta sannan a zuba man zaitun, idan ya yi zafi sai a zuba albasa sannan a yi ta juyawa kamar na tsawon minti bakwai sannan a zuba kori kamar cokali biyu na cin abinci, sai a ci gaba da juyawa na tsawon minti daya.

Sannan a zuba tafasashiyar madara a cikin hadin tare da ‘cream’ da gishiri da magi da kuma yankakken timatir kanana sosai sai a ci gaba da juyawa.


A dauko kazar da aka riga aka daddatsa a zuba a cikin miyar sannan a rufe na tsawon minti biyu kacal sannan a sauke. Za a iya sanya ganyen kori idan ana da bukata. A tafasa farar shinkafa sannan a dauko hadin miyar Indiyawa a zuba a kan shinkafar tare da hada shi da jus din lemun zaki. Hmnnn! A ci dadi lafiya

Post a Comment

Previous Post Next Post