Balaga

*Balaga*

Irin sauye sauyen da ke faruwa a lokacin balaga,
suna faruwa ne yau da gobe a jikin kowane
matashi, yawancin lokuta daga shekara takwas,
kuma sun bambamta daga mutum zuwa mutum.
Balaga shine lokacin da yaro ko yarinya ke zama
cikakken mutum. A wannan lokacin, al’aurar su
na kara girma, kana jikinsu na zama a shirye
domin haihuwa. Yayin da mutum ke balaga,
jikinsa na sakewa nan da nan. Wannan na iya sa
wa mutum ya zama cike da damuwa ko kuma
zumudi. Wadannan sauye sauyen na iya sa wa ka
rika takama, kana murna; amma kuma suna iya
sa ka rikice, ko kuma ka rika jin kunya, da dai
sauransu. A wannan lokacin ne watakila abokai
da dangi, sa’anni da kuma sauran mutane zasu yi
kokarin shirya yadda ya kamata a yi rayuwa. Alal
misali, zasu so su tsara tabi’ar ka, da yadda ya
kamata kamannin ka su kasance, da kuma irin
mutanen da za ka yi cudanya da su. Dukan
wadannan, zabi ne mai mahimmanci da ya kamata
ka yi. Za ka iya yin haka ta hanyar yin
tattaunawa, da neman bayyani, da kuma a wasu
lokutan ka yi wa kan ka wasu tambayoyi masu
wuyar amsawa

Post a Comment

Previous Post Next Post