Haila ga mata

*Haila*

Ana haihuwar yara mata da wasu kwayaye biyu
(ovaries) wadanda ke kunshe da dubban kwayayen
da ba su nuna ba (duba shafi a kan Halittar jikin
namiji da macce). Bayan yarinya ta balaga, a
kowane wata tana sakin kwai daya da ya nuna.
Ana kiran wannan ‘saukar kwai’ (ovulation),
kuma wannan na faruwa wajejen kwana goma sha
hudu kamin soma al’ada. Idan kwan bai hadu da
maniyyi ba sai ya mutu. A kowane wata mahaifa
na shirya wa yiwuwar daukar ciki, kuma fata ta
cikin mahaifa na zama da kauri da kuma taushi.
Idan jikin macce ya gane cewa ba maganar daukar
ciki, sai fatar da ke cikin mahaifa, tare da kwan
su zama haila su fice ta farji. Ba za a iya ganin
kwan ba saboda ya cika kankanta. Ana fara kirga
lokacin haila daga ranar da aka fara, zuwa
jajibirin ranar da za a fara wata al’adar.
Zagayowar al’ada na canzawa, don zai iya
kasancewa kwana ashirin da daya ko kuma ma zai
iya kai wa kwana arba’in. Idan macce na al’ada,
tana iya amfani da tawalin al’ada ko kuma fad,
ko audugar al’ada don ta tare jinin da ke zuba.
Kina iya yin amfani da littafin tsarin lokaci watau
diary domin sanin lokacin da za ki fara al’ada. Ba
dukan mata ne ke yin al’ada a kan lokaci ba, kuma
lokacin fara al’ada ya bambanta. Wasu ‘yan matan
na farawa tun da wuri (alal misali tun suna da
shekara takwas), yayin da wasun ke dadewa basu
fara ba. Haka ma, tsawon lokacin da ake dauka
ana hailar ya bambanta daga macce zuwa macce.Yawanci suna yin kwana biyar zuwa bakwai.
Amma kuma wannan na iya sauyawa, don a wasu
lokutan ba a kaiwa kwana biyar. Da zarar yarinya
ta fara al’ada, zai dau lokaci kamin jikin ta ya
saba. A shekarar farko mai yiwuwa ta ketare wata
daya ko fiye da haka bata ga haila ba. Amma yau
da gobe jikin nata zai saba.
Irin canjin da ake samu na yawan sinadarin
(hormone) da jikin macce ke samarwa kamin
lokacin yin al’ada, ko kuma a lokacin al’adar, mai
yiwuwa ya shafi halin da macce zata nuna, ko
kuma abinda zata ji a ran ta. Mai yiwuwa ta ji
karin kuzari, ko kuma ta ji tana sha’awar namiji,
ko kuma ran ta ya baci, ta ji kamar ta yi kuka,
ko kuma ta rika yawan fushi a lokacin saukar
kwai ko kuma jim kadan kamin ta fara haila.
Mai yiwuwa nonunan ta su rika ciwo ko su kara
girma; kuma a wasu lokutan wasu kananan
kuraje kan fito a fuska. Wasu matan sun dara
saura jin bambam a jikinsu a lokacin da suke
haila. Kuma wannan na iya sauyawa a rayuwar
macce. Ta haka ne mata ke sakin kwayaye har
zuwa lokacin da suka daina haila. A yawancin
lokuta hakan na faruwa idan macce ta kai
karshen shekaru arba’in zuwa hamsin. Bayan
wannan lokacin, ba zata kara yin al’ada ba, kuma
ba zata dauki ciki ba.
 

Post a Comment

Previous Post Next Post