Hanyoyin Hana daukar cikin na mata

*Hanyoyin hana daukar ciki na mata*
maganin da za a sha: kwayar hana daukar ciki mai
kunshe da sinadaran da ke hana kwayayen nan biyu
(ovaries) sakin kwai daya a kowane wata.
yadda za a sha: yawancin lokuta ana shan kwayoyin
har tsawon kwana ashirin da daya, kana a daina sha har
kwana bakwai. Macce na iya barin shan kwayoyin duk
lokacin da ta ke so, idan tana son ta yi ciki.
alfanun kwayoyin hana daukar ciki: suna da saukin
amfani, watakila su rage zafin al’ada, mai yiwuwa kuma su
hana kamuwa da wani nau’i na kansar mahaifa ko farji.
illar magungunan hana haihuwa: dole ne a sha su kullum,
ba sa hana kamuwa da cututukan da ake dauka ta
hanyar jima’i ko kuma kwayar cutar HIV; matan da ke
shan maganin hana haihuwa suna kuma shan taba, sun fi
fuskantar kamuwa da ciwon gudajin jini da ke hana jinin
gudawa a jijiyoyi (thrombosis), da kuma ciwon zuciya

Post a Comment

Previous Post Next Post