HADIN lalle me maroon

(HADIN LALLE ME MAROON)🌹

Hadin Lalle Kala Kala Ne Kamar Yanda Maroon Dinma Kala Kala Ne
Akwai me Haske Akwai Me Duhu,Me Duhu ma Kala Kala ne, Me Hasken Ma Kala Kala Ne.
Kunga Kenan Kowanne Da Kalan Hadin Sa.
Kuma Nayi Niyan Fadane Domin Kowa Ma Ya qaru Ba Inda Akace Ka Boye Sani,in har ka sanin, Kuma Kowa a Rayuwannan Rabon Sa Yake Ci, Wllh Baxa ka Taba cin Abinda Ubangiji be Qaddara Naka Bane,Yanda Idan Ka Tambaya Kowa Bayasan Fadama.

Wannan Hadin Bagaruwa ne
Da Farko 
Zaki Samu Lalle Na Gargajiya me kyau, Kore me kamu,
Dan Da Lallan Gargajiya ma inde me kyaune,Yafi,
In Kuma Baki samu ba
Ki samu 
Lallan Zarah
Ko Alwaradah (Wanda Wasu Suke Cewa Red Rose)🌹

Xaki Samu
Bagaruwa
Tsamiyya
Zobo
Suger 
Muhallabiya

Ki zuba ruwa Dede a wuta kisa Bagaruwa,Tsamiya, Suger,Sannan Gishiri Kadan, ya tafasa sosai
Ki sauqe ki Tace shi

Ki qara mayar dashi wuta
Sannan ki zuba Gishirin Lalle,Kadan 
Ya qara Tafasa Kadan Ki Sauke,

Wannan Hadin Yana Iya Kai Almost 2 month kina amfani dashi

Sannan ki kwaba Lallen Da Wannan Ruwan Da Kika Dafa,
Se Muhallabiya me kyau da Sugar, 
2 Hours before kisa
Bayan kin kwaba ki samu Leda kisa a ciki yayi 2 hours 

Se kisa,
Insha Allah Xeyi Maroon Sosai

Bagaruwan Bada Yawa Ba Kadan,
Sbd Idan Yayi Yawa Yana Sawa Daga Baya Ya Miki Tabbare² Baki,

Dik Wacce Tayi Ya Mata, Dan Allah Ta Min Addu'ah
Ubangiji Allah Ya Biyamin Buqatuna Na Alkhairi,
Ya Bani Miji Na Gari
Idan Kuma Ba Alkhairi bane Ya Musanya min da Wanda Ya Fishi Alkhairi 🤲,,,,,,,,,,,.

Post a Comment

Previous Post Next Post