shin mene gaskiya gama da halittu aliens

Shin menene Gaskiya Game da Halittun ALIENS? 
01
Gawani Dan karamin theory da na karanta akansu 
In akwai Mai wani Karin bayani Sai ya Mana 
ALiens 
Sufa aliens dama tun can akwai su hallitu ne na allah masu kama da mutane sak ammafa ba mutane bane 
Kuma idan sukayi aure da dan adam ko sukayi jima'i dashi basa iya haihuwa.

Kuma suna zuwa cikin wannan duniya tamu daga wata unguwa ta taurari da ake kira erra jinsin da suka fi sauka a wannan zamani a cikin duniya sune jinsin gray aliens.
 
Tun can dama aliens suna zuwa cikin duniyar mu amma inda suka fi bayyana shine wasu sassa na pyramid na giza dake Egypt da america da asia  da wasu sassa yan qalilan na Africa ciki harda Nigeria shekaru kamar 15 sun bayyana a wani kauye mai suna dulali dake karamar hukumar darazo ta jahar Bauchi  sannan sun ta6a bayyana a jahar cross river.

Suna da masifar wayo da hangen nesa sannan suna da tsananin fasahar technology da ilimi sanin yanda duniya zata iya kasancewa nan gaba da halin da zata iya fadawa mafi shaharar hanyar su ta sufuri shine suna da jirage da ake kira UFO wanda suke kera shi da tsantsar fasa mai tsanani da sarkakiya kuma yana da kira kamar faranti ko cycle kodai nace da'ira yana da mutukar azababben gudu kamar walkiya.

Kuma sunfi dan adam hadari da iya shege a cikin yan mintina zasu iya tashin nahiya guda shi yasa masana suke ta bincike ba dare ba rana wajen kera makaman da za,a iya amfani dasu dan kota kwana sabida tsaro badan tsoro ba.

Sabida bincike ya tabbatar da nan da shekaru 30-50 ko sama da haka zasu mamaye duniya a ringa rayuwa da su dan suna iya rayuwa da mutane idan baka sani ba sai kace suma mutane ne basu fiye cutar da dan adam ba sai ta kama dan sunfi mutane karfi sosai da dabaru ga basira

Amerikawa suna yawan yin fina finai na aliens karka dauka babu su akwai su daga cikin films din akwai wani film mai suna aliens Quarantine da makamantan su.

Post a Comment

Previous Post Next Post