[4/15, 9:17 AM] +234 813 420 3941: Assalamu alaikum
Barkanmu da safiya, fatan mun wayi gari cikin koshin lafiya ya ibada. Allah ya karba mana baki daya
In sha Allahu zamucigaba da karatunmu
[4/15, 9:19 AM] +234 813 420 3941: *JANA’IZ.*
Mutum babu makawa koda ya yi rayuwa mai tsawo sai ya mutu.
Za’a dauke shi daga gidan aiki (wato nan duniya) zuwa gidan sakamako (wato lahira), yana daga cikin hakkin musulmi da ya gai da shi idan bai da lafiya, kuma ya shaidi janazar sa idan ya mutu.
An sunnanta gaida mara lafiya da kuma tunatar da shi yin tuba da wasiyyah.
[4/15, 9:21 AM] +234 813 420 3941: An sunanta a fuskantar da wanda mutuwa ta halarto mishi da ga alkibla, sai a sanya shi maralafiyan a gefen daman sa da fuskar sa, hakanan idan ba zai cutu ba, in bahaka ba sai juya shi ya dubi sama kafarsa na fuskantar alkibla, sai a daga kansa sama kadan don ya fuuskanci alkiblla, sa’annan a lakana masa “Kalmar shahada”, sai a zuba masa ruwa a makogwaronsa ko wani abin sha, kuma a karanta masa Suratul Yasin.
· Idan mutum musulmi ya rasu, an sunnanta rufe masa ido, da hada masa gemunsa da hada masa kafafun sa da hannuwansa, a kuma dauke shi daga kasa, a cire masa tufafin sa a kuma rufe masa al’aurasa, a dora shi akan gadon wanka yana kwance gefen dama, kuma yana mai fuskanta alkibla in hakan ya sawwaka in ba haka ba sai a juya kafarsa suna masu fuskantar alkibla.
[4/15, 9:23 AM] +234 813 420 3941: *Wankan mamaci.*
Mutanen da ya kamata su wanke mamaci su ne wadanda shi mamacin ya yi wasiyya da su, sa’annan baban sa, sa’annan kakan sa, sa’annan na kusa. Ita kuma mace wacce ta yi wasiyyah, sa’annan mahaifiyarta, sa’annan kakarta, sa’annan na kusa da ita, haka kuma kowanne mauraci (miji) zai wanke matar sa, ita kuma ta wanke shi wadanda suke musulmi.
An yi sharadi mai wanka ya kasance mai hankali, mai wayo masani game da hukunce hukuncen wanka.
An haramta musulmi ya binne kafiri ko ya wanke shi, saidai yana iya tura masa kasa idan babu wanda zai yi hakan.
[4/15, 9:25 AM] +234 813 420 3941: *Siffar wanka na sunnsa ga mamaci.*
Idan za’a yi wa mamaci wanka, sai a rufe masa al’aura, sa’annan a daga kansa zuwa kwatankwancin yadda zai zauna. Sai a matsa cikin sa kadan-kadan sai a zuba ruwa mai yawa, sa’annan ya sa wani kyalle a hannunsa sai yayi masa tsarki, sa’annan ya yi masa alwala, sa’annnan ya yi niyyar wanke shi, sai ya wanke shi da ruwa da magarya ko sabulu, zai ya fara daga kansa da gemun sa, sa’annan sa’annan gefansa na dama, sai kuma gefansa na hagu, sa’annan ya wanke shi sau biyu zuwa uku kwatankwacin yadda ya yi na farko, in bai tsarkaka ba sai ya ta wanke wa har sai ya tsarkaka, sai ya sanya wankan karshe ya zama ruwa da kafur ko turare, in kuma ya kasance gashin bakin sa ko kunba sa suna da tsawo sai a debe su, sa’annan a tsane shi da tufafin. Ita kuma mace ana yi mata kamu uku na gashin kanta sai a sake su zuwa baya.
[4/15, 9:29 AM] +234 813 420 3941: *Likafani.*
An sunnanta ayi wa namiji lifafa (likafani) farare guda uku, sa’annan a shinfida su akan juna a sanya musu turaren hamuta, sai kuma a sanya gaurayayyan turare a tsakanin lifafa, sa’annan a sanya mamaci a cikin su. Sai a sanya auduga a ramukan (kamar dubura) sai a daure masa daga sama wani kyalle kamar gajeran wandao don ya rute masa al’auran sa, sai a sa masa turare a sauran jikinsa. Sa’annan a sakko da gefan likafanin dake sama a daga bangaren hagu a maida gefen dama, sa’annan a sakko da gefan likafanin dama akan hagu, sannan shi ma na biyun haka za’a yi shi, hakanan ma na ukun haka za a yi shi, sai a sanya abun da ya sausa a gefan kan sa, sai a daure a gicciya sai kabari za’a kwance.
Za’a iya yi wa karamin yaro lifafa daya, kuma ya halatta a yi masa ukun.
Ita kuma mace ana daura mata zani sa’annan a sanya mata riga, sai kuma a daura mata kallabi (dankwali) da kuma riga, bayan an nade ta a lifafa biyu sai a sanya mata riga a yi mata kallabi kuma da dankwali, sa’annan kuma a nadeta da lifafa biyu. Amma yarinya karama a sa mata riga da lifafa biyu.
- Ya halata a wanke mamci mace ko na miji sau daya, wanda zai game jikin shi gaba daya, haka lifafa daya wacce za ta rufe dukkan jikin shi.