[4/14, 9:17 AM] +234 813 420 3941: *SALLAR ROKON RUWA.*
Hikiomar sharanta ta.
Alllah ya halicci mutum kuma ya kagi halittar sa akan yadda zai maida tamari gareshi da neman mafaka a gareshi a lokacin saukar bukatun sa. Ko lokacin da fituntunu suka kawaye shi, rokon ruwa abune wanda yake bayyane daga cikin abubuwa wadanda suke a bayyane a cikin tunanin mutum wanda Allah yasa musulmi ke maida lamarin sa gareshi don neman ruwan sama.
[4/14, 9:20 AM] +234 813 420 3941: *Ma’anar ta.*
Shi ne neman shayar wa daga Allah madaukakin sarki ga kasa da bayi, hanayar yin sallah da addu’a da kuma neman gafara.
*Hukuncinta.*
Sallar rokon ruwa sannah ce mai karfi, Manzon Allah ﷺ ya yi, kuma ya shelanta ta a cikin mutane, kuma mutane suka fito domin gabatar da sallar a filin idi sallah.
*LOKACINTA, DA KUMA SIFFARTA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA.*
Kamar sallar idi take.
An so limami ya sanar da yin ta kafin lokacin da wasu kwanaki.