najasa

 Assalamu alaikum

Barkanmu da safiya, fatan mun wayi gari cikin koshin lafiya ya ibada. Allah ya karba mana baki daya

In sha Allahu zamucigaba da karatunmu
 *NAJASA*

Ma’anarta a yaran Larabci da kuma shari’ah.

 Najasa a yaran Larabci ita ce; Kazanta, kuma abu mai najasa kazanta ne, wannan abun ya zama najasa kuma ya gauraya da najasa.

 Ita najasa a mahangar Shari’ah aba ce wadda aka kaddara, tana hana jiki yin sallah kamar fitsari, jini da giya.
 *Nau’ukan najasa biyu ne;*

I. Ayyana (Bayyananniya).

II. Hukmiyya, (wato a hukunce).
 *Ayyana: Ita ce abinda yake shi karankanshi najasa ne, kamar kare da alade. Wanda ba’a tsarkaketa da wankewa a wannan halin.

*Hukmiyya: Najasa ce wacce ta afkawa wuri mai tsarki.
Rabe-raben Najasa:-* Najasa ta rabu kashi uku.

1. Kashin da yake an yi ittifakin najasar sa.

2. Kashin da yake an yi sabani akan najasarta.

3. Kashin da yake najasar ne amma an yi afuwa akai.
 *Kashin da yake an yi ittifakin najasar sa.*

1. Mataccan duk abinda yake rayuwa a bayan kasa. Amma wanda ke rayuwa a ruwa to mai tsarki ne kuma halal ne.

2. Jinin yanka, wato wanda ya kwarara a lokacin da ake yanka dabbar da take mai rayuwace a bayan kasa.

3. Naman alade.

4. Fitsarin mutum.

5. Kashin mutum.

6. Maziyyi.

7. Wadiyyi.

8. Naman abinda bai halatta a ci ba cikin dabbobi.

9. Da abunda aka yanke ko aka cire daga jikin dabbar tana lokacin tana raye.

10. Jinin al’ada.

11. Jinin haihuwa. (wato jinin biki).

12. Jinin istihala. (wato jinin cuta, wanda ba na al’ada ba, ba kuma na biki ba).
: *Kashin da yake an yi sabani akan najasarta.*

1. Fitsarin dabbar da ake cin naman ta.

2. Kashin dabbar da ake cin naman ta.

3. Maniyyi.

4. Yawun kare.

5. Amai.

6. Mataccan abun da ba shi da jini a cikinsa, kamar zuma, kenkyaso, da kudin cizo da kuma makamantan su. *Kashin da yake najasar ne amma an yi afuwa akai.*

1. Ruwan dagwalon kan hanya.

2. Jinin da yake kadan.

3. Jini da ruwan kurji na mutum ko dabba, wacce ake cin naman ta.
 *Yadda ake tsarkake najasa.*

Tsarkake najasa yana tabbata ne da wanke ta, ko yayyafa ruwa, ko kuma cudawa da shafawa.

* Tsarkake tufafi mai najasa; Idan najasar ta kasance ta daskare to sai a kankareta sannan a wanketa, idan kuma danya ce sai a wanke kawai.

* Tsarkake fitsarin yaro: Ana tsarkake fitsarin yaro ne ta hanyar yayyafa masa ruwa, idan bai fara cin abinci ba. Ana tsarkake najasa dake akan kasa, ta hanyar gusar da ita, sai azuba ruwa akan najasar. Kuma ana tsarkake takalmi ta hanyar goge shi a kasa ko da tafiya a wuri mai tsarki, kuma ana tsarkake abubuwa kamar kwalba, wukake da ire-iren su ta hanyar gogesu, kuma idan kare ya yi lallago (wato ya sa baki) a kwarya ana wankewa ta ne sau bakwai daya daga ciki za asa turbaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post