*Lokuttan sallaloli biyar:-*
Sune abun da aka cirato daga taukit, kuma shi ne iyakancewa, lokacin sallah sababine game da wajibcin ta, kuma sharadi daga cikin sharuddanta.
Hakika Annabi ﷺ ya iyakance lokutan sallaloli biyar a hadisai masu tarin yawa. An karbo daga Dan Abbas Allah t, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: “Jibril ya limanceni a daidai Ka’abah sau biyu”. Sai ya ambaci lokutan salloli biyar, sa’annan ya Manzon ﷺ Allah ya ce; “Sai Jibril ya juya sai ya ce dani; Ya Muhammad wannan shi ne lokucin Annabawa kafin kai, kuma lokuci shi ne abinda ke tsakanin wadannan lokutan biyu”. {Abu DawuHakika lokutan salloli biyar sun zo ne a yadda suka raba yini da dare. Idan mutgum ya yi barci gwargwadon iko to hakika zai say a sami hutu, dab da asubahi kum lokacin kokari da kuma aiki, lokacin sallar asubahi kuma ya yi, domin mutum ya ji ya iya banbace shi da sauran hlittu, ka ga sai ya fuskanci yininin nasa da guzurin imani.
Kuma lokacinin da ya fuskanci yini sai ya sake tsayawa domin ya yi lura da sha’anin Ubangijinsa a sallar azahar, tare da inganta aikin sa a farkom yinin sa, sa’annan idan la’asar ta zo sai ya sallace ta, yana mai fuskantar sauran yinin sa, sa’annan magaribi domin fuskantar dare da kuma isha’i a tsakiyar daran yana dauke da su a cikin darensa, wanda yake wurine na boye haske da shiryawa ga hanya madaidaciya. Kamar yadda sallah ta kasance tana da lokuta mabanbanta, wannan zai taimaka wa mutum domin yin tunani a cikin mulkin Allah madaukakin sarki da kum kyauta ta ga duk abunda yake kiyaye shi mutum na dare da yini.
*Lokacin Sallar Azahar.*
Farkon lokacin zuhur yana farawa ne daga zawali ne, shi ne kuma gushewar rana daga tsakiyar sama. Karshen lokacinta, idan inuwa ta yi daidai da tsawon kowannne abu bayan inuwar da ta karu ta gushewar rana (alokacin azahar).
[ *Lokacin sallar Lasar.*
Farkon lokacin sallar lasar, daga kaiwa karshen lokacin azahar ne. lokacin da inuwa ta yi daidai da tsawon kowanne abu bayan inuwar da ta karu alokacin azahar wato inuwar gushewa. Karshen zabbaben lokacita kuwa shi ne lokacin da inuwa ta ninka kowanne abu sau biyu. Lalurin su shi ne faduwan rana.
*Lokacin sallar magariba.*
Farkon lokacin sallar magariba shi ne faduwau rana. Karshen lokacin magariba kuwa shi ne bayyanar taurari, karshen lokacin halascin sallatar magariba kuwa tare da karhanci shi ne boyewar jan shafaki.
*Lokacin sallar isha’i.*
Farkon lokacin sallar isha’i shi ne boyewar jan shafaki. Amma karshen lokacin shi ne tsakiyar dare.
*Lokacin sallar asubahi.*
Tags:
TARBIYYA MUSULUNCI