ALWALA

 *ALWALA.*

(a) Ma’anar alwala; Ita ce amfani da ruwa mai tsarki akan gabobi huda akan kuma wata siffa kebantacciya a Shari’ah’.

(b) Falalar alwala: Abin da aka ruwaito daga Annabi (ﷺ‬) yana nuna falalar alwala hakika ya ce; “Babu daya daga cikinku da zai yi alwala ya kuma kyautata alwalarsa sa’annan ya ce; “Ina shaida babu abin bauta wa da cancanta sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, kuma ina shida wa lalle Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, take an bude masa kofofin aljannah guda bakwai ya shiga ta inda ya keso”. (Muslim ya ruwaito).

Abun nufi da kyautata alwala a gabbai shi ne, yin amfani da ruwa ba tare da barna ba, wanda hakan yake tabbatarwa masu yin haka su kasance masu hasken fuska da gabubuwa masu walkiya ranar kiyama, akan fadin Manzon Allah (ﷺ‬) cewa: “Lalle al’ummata za su zo ranar tashin alkiyama suna masu hasken fuska, da walkiyar gabbai na daga alamar alwala, saboda haka duk wanda ya samu ikon tsawaita hasken sa sai ya aikata”. (Bukhari da Muslim).
 *Sharuddan alwala guda goma ne:*

1. Musulunci.

2. Hankal.

3. Wayo.

4. Niyya, tare da kyautata hukuncinta tare da niyyar ba zai yanke ta ba har sai ya kammala alwalar.

5. Daukewar abunda ke hana alwala (Jinin al’ada da jinin biki).

6. Istinja’u ko istijmaru.

7. Ruwan ya kasance mai tsalki.

8. Ruwan ya kasance na halsta.

9. Gusar da abunda zai hana shigar ruwan fata.

10. Shigar lokaci ga wanda ke da hadasi a kowani lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post