wankan janaba

 *WANKA.*

Ma’anar wanka; A yare da kuma wurin mallaman fikhu, Alghuslu (غُسل) da wasalin dumma ruwan da ake wanka da shi ne, amma da wasalin fataha (غَسل) aiki ne (wato yin wankan) da wasalin kasra (غِسل) kuma shi ne darasin mu, watau tsarkakewa.

Ma’anar shi a shari’ah: shi ne zuba ruwa a dukkan jiki, daga tsakiyar kai har zuwa kasan diddige da ruwa mai tsarki akan sifa kebantacciya. Mace da namiji wajan siffar wankan su dayane, saidai ga mace a lokacin da take wankan daukewar jinin al’ada ko na biki, to yana kamata a gare ta da ta wanke alamar jinin domin tsarkaketa da kuma kauda warin jinin.
[ *Abubuwan dake wajabta wanka.*

Abubuwan dake wajabta wanka guda shida ne:-

1. Fitar maniyyi kai tsaye, ta hanyar jin dadi daga mace ko namiji.

2. Boyewar kan azzkari a cikin farji.

3. Idan mutum ya mutu ya wajaba ayi masa wanka, saidai in shahidi ne.

4. Musuluntar kafiri ko wanda ya yi ridda.

5. Jinin al’ada.

6. Jinin biki (wato jinin haihuwa) *Daga cikin wankan da suke an so a yi su a musulunci.*

1. Wankan jumu’ah.

2. Wankan shiga harami (da hajji ko da umarah).

3. Wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka.

4. Wankan idi biyu (na zuwa karamar sallah da babbar sallah).

5. Idan mutum ya farfado daga hauka ko farfadiya.

6. Wankan shiga Makkah.

7. Wanka domin sallar kisfewar wata ko kuma rokon ruwa.

8. Wanka na mai istiha a kowacce sallah.

9. Ga kowanne jima’i an so a yi wank *Sharuddan wanka:*

1. Daukewar abinda ke wajabta wanka, (kamar al’ada…).

2. Niyya.

3. Musulunci.

4. Hankali.

5. Wayo.

6. Ruwa mai tsarki kuma halstacce.

7. Gusar da abunda ke hana shigar ruwa zuwa ga fatar jiki.
 *Wajiban wanka:*

 Wajiban wanka su ne yin Basmalah, an dauke wa mutum idan ya manta, amma ba’a barinta da gangan ba.

*Farillan wanka:*

Niyya, da game jiki da ruwa gabadaya, da cikin bakin sa, da hancin sa, amma yana wadatar da shi kan mafi galibin zato. Duk wanda ya yi niyyar wanka na Sunnah ko wajibi, to daya daga cikin su ya wadatar da shi akan dayan, (kamar wankan janaba ya wadatar da na juma’a).

 Wanka daya ya wadatar ga mai al’ada da janaba lokacin da ta yi niyya daya.
 *Sunnonin wanka:*

1. Basmallah (wato fadin:بسم الله ).

2. Farawa da wanke kazanta.

3. Wanke tafukan hannu.

4. Alwala kafin wanka.

5. Damantarwa.

6. Jerantawa.

7. Goga hannu a sauran jiki, (cuccudawa).

8. Mai-maita wanke kafafuwa a wuri na daban.
 *Makaruhan wanka:*

1. Barnata ruwa.

2. Wanka a wuri a wuri mai najasa.

3. Wanka ba tare da wani shamaki ba ko wani abu makamancin haka.

4. Wanka a ruwa mai gudana.

*Abubuwan da ke haramta ga mai janaba.* An haramta mishi;

1. Sallah.

2. Dawafi.

3. Daukar Alkur’ani ko shafashi, sai dai in bango ne.

4. Zama a masallaci

5. Karatun Alkur’ani.

Post a Comment

Previous Post Next Post