pepper soup

*OFFALS PEPPER SOUP (PERPESUN KAYAN CIKI) By Gloden KITCHENπŸ‘¨πŸΎ‍πŸ³πŸ‘©πŸΎ‍πŸ³πŸ²πŸœπŸπŸ›πŸ₯£*

Abubuwan buqataπŸ‘‡πŸΎ
Kayan ciki
Attarugu
Tattasai
Albasa
Sinadarin dandano(Maggi's)
Curry
Thyme
Mai 
Irish 
Ginger
Garlic

Da farko zaki wanke kayan cikin tas ki tabbatar kin wanke shi tmya fita sosai,sai ki Zuba a tukunya,ki jajjaga attarugu da tattasai ki Zuba akai,ki jajjaga citta da tafarnuwa ki Zuba akai,ki saka thyme,curry,sinadarin dandano,mai kadan (ba a saka mai da yawa,saboda idan girkin ya soma tafasa mai zai rika futowa a jikinsa a hankali,idan har aka Saka masa mai da yawa,ya zo ya fitarda man jikinsa,girkin ba zai ci yu ta dadi ba saboda mai zai masa yawa)...
Ki zuba ruwa daidai Wanda zai dafa maki kayan cikin,sai ki Dora kan wuta ki dafa,idan ya tafasa zaki ji kamshi ya soma tashi,a gefe daya zaki fere dankalin kamar guda5 Sai ki yanka shi manya (kamar ki tsaga kowanne gida4) ki wanke ki ajiye gefe daya.ki yanka albasarki ki ajiye gefe,idan Naman ya dahu kamar 3/4 Sai ki Zuba yankakken irish naki tare da albasa akai ki Dan juya su,ki rife like for 10-15mins shikenan ki sauke. Kin kammala Sai ci.
Zaki iya cin gurasa,sinasir,waina,bread da wannan dabgen tare da romonsaπŸ˜‹.

gloden 

Post a Comment

Previous Post Next Post