Zuwa gareku sabin aure (1 month to 5years) da masu niyyar aure nan kusa.....Ku sani dukkan ku biyu 'yan koyo ne a babin aure da zamantakewar sa. Abunda kuka sani ko kukaji ba lallai ku tarar a auren ku ba dan kai daban, itama daban, kuma baku zama daya da sauran ma'aurata ba.

Zuwa gareku sabin aure (1 month to 5years) da masu niyyar aure nan kusa.....

Ku sani dukkan ku biyu 'yan koyo ne a babin aure da zamantakewar sa. Abunda kuka sani ko kukaji ba lallai ku tarar a auren ku ba dan kai daban, itama daban, kuma baku zama daya da sauran ma'aurata ba. 

Ku kasance masu HAƘURI da yima juna UZURI dan dukan ku 'yan koyo ne a harkan zamantakewar aure. 

Ya kai miji, Ka sani a gidan su bata san ya lura da gida a matsayin matar gida yake ba, mahaifiyarta ke dawainiyoyi da dama da bata san ya akeyi managing din su ( emotionally, mentally or physically) ba, dan bata kai ta san su ba, ta iya su ko tayi su dan ba nan ya dace tayi ko tasan su ba sai dai a gidanta. 

Ka sani kusan abubuwa da dama a gidanka zata koya kuma ta aiwatar, yadda ake hakuri da lura da miji, yadda zatayi maka magana ko ta mu'amalance ka, yadda zata lallashe ka, ko ta kyautata ma, haka zai sa sai ka mata hakuri da uzuri akan kurakuran da zatana maka har zuwa lokacin da zata goge itama dan ba abunda zata iya lokaci guda bane. 

Ya ke mace :- Kema ki sani, shi kan sa wadda kika aura dan koyo ne a harkan lura, riqe gida da mata. kafun aure shima mahaifin sa ke komi ko kusan komi a gidan su bashi ba. Tabbas akwai abunda ya sani ko yake yi, sannan akwai abunda kuma bayayi dan bai kai yayi su ba ko yasan su dan shima  ba wajen da ya dace ya sani ko yayi bane sai a gidan sa da kuma matar sa. 

ki sani yanzu zai koyi kincikon gida, lura da al'amuran rayuwar ki, na shi da yaran da zaku haifa, yanzu zai koyi irin su yanke hukunci, hanyar gyara matsalolin ku ko na gida duk, wadannan abubuwa ne da sai sun sami mutum yake gane yadda zai gudanar dasu dan abune da ya shafeku da rayuwar auren ku kadai. 

Ku sani, in kukayi aure tamkar jarirai/yara kuke da ake tsammanin nan gaba ku girma ku zama mutune, amma kafun ku girma ku zama mutane dole sai kunbi matakai na girma kamar kowani yaro wato a hankali zaku soma koyan zama a koyon zaku gungura ta gaba, ta baya da ta gefe, a hankali zaku soma koyon rarrafe ko jagindi, a koyon rarrafen zaku tuntsura, zaku buga baki ko goshin ku, a hankali zaku koyi tsayiwa, a tsayiwan nan kun dinga faduwa kuna tashi, a hankali zaku soma takawa kuna tafiya daya daya, nan ma kun dinga faduwa kuna tashi, a hankali har tafiyar ku ta miÆ™e kuna yinta cikin shauqi da rashin fargaba wadda  in kuka girma har sauya ta kuke yadda kuke so.

 Sai dai duk da kun kware a tafiya, baya hana watarana kuyi tuntube ko ku buge ko  ku faÉ—i, amma faÉ—uwar baya hana kuji zafi, kuma baya hana ku yi hakuri da zafin sannan ku tashi ku ci gaba da tafiyan har illa ma sha Allah. 

Haka shi rayuwar aure yake a hankali ake koyo har a goge a ciki, lokaci da shekaru ke sa mutum ya gane ragamar zaman cikin sa,  kuma duk jimawa da iya shi ba zai  hana a yi ko a ga abunda ba'a so ba. 

Karku manta ita rayuwar aure makarantace da kullum sake sabon karatu ake kuma ba ranar qarashi matuqar a na cikinnsa, dan ko an chanza aji za dai a cigaba da sabon karatun ko É—ori daga inda aka tsaya. 

✍️ Fatimah Chikaire

Post a Comment

Previous Post Next Post