yadda ake hada lomen ayaba da Kwa Kwa

Yadda ake hada lemon ayaba da kwakwa

Kayan hadi
 
•Ayaba
•Kwakwa
•Sukari
•Ruwan kwakwa
•Madara
•Filebo

Yadda ake yin hadin

Da farko uwargida za ki tsiyaye ruwan da ke cikin kwakwarki, ki ajiye shi a gefe guda. Sai ki kankare bakin bayan kwakwar sannan sai ki wanke ta. Daga nan sai ki yanyanka kwakwar kanana sannan sai ki zuba a bilenda ki kawo ruwan kwakwar nan ki zuba akai sai ki markada.
 
Idan ki ka tabbatar ya markadu sai ki sami mataci ki tace za ki iya kara ruwa kadan akai. Idan kika gama sai ki ajiye ruwan kwakwar a gefe.

Sai kuma ki dauko ayabarki ki yanyanka ta kanana sai ki zuba ruwan kwakwar nan da kika tace a cikin bilendar sannan ki zuba ayabar nan akai sai ki markada. Idan kika tabbatar ya markadu sai ki sami babban kofi ki juye a ciki sannan ki dauko sukari da madara ki zuba akai sannan sai ki dauko filebo mai dandanon kwakwa ko ayaba ki zuba don ya kara fito wa lemon dandano.

Post a Comment

Previous Post Next Post