BURIN MACE KO NAMIJI GAME DA ABOKIN RAYUWAR AURE

BURIN MACE KO NAMIJI GAME DA ABOKIN RAYUWAR AURE

Ko wace macen da takai munzalin aure,kololuwar burin ta a rayuwa shine,taga ta auri mutumin kirki wanda yake kwatan ta koyi da tafiya bisa tafarkin manzon tsira SAW wanda take sa ran zai kwamta ta ui mata adalci da kyautata mu'amala gare ta a ya yin da suka yi aure.
To amma son hakan a zuci ko kuma fadar sa da baki kodai ba zai isa ba wajen samun cikar wancan burin nata matsawai dai ba ta hada da aiki tukuru bisa juriya da jajircewa ba.
A matsayinki ta mace ko da ace kin yi sa'a Allah ya azurta ki da irin wancan abokin zaman da kike bukata,to fa sai kin yi aiki tukuru kafin ki iya canjawa ko dora wannan miji naki bisa turbar da wannan auren naku zai bun kasa har ya kai ga nasarar da kike bukata.

Kisa a ranki cewa ba zaki taba samun abinda kike so daga wajen mai gidan ki ba har sai kin zauna kinyi sabon karatu mai zurfi akan sa yadda zaki masa fahimta irin ta ciki da waje.
Kuma irin wannan karatu ya sha bambam da duk wanda ki kayi masa a baya kafin ku yi aure,domin duk yadda kike tsammanin kin shaku da shi saboda kusanci na soyayyar data gabata kafin aure,to daga sanda aka daura aka shigo gida,to fa karatu ya dawo sabo,ki kaddara cewa a baya baki san shi ba yanzu ne zaki san ainihin waye shi.

Da zarar kin fahimci irin kalar mai gidan naki,ba tare da wata-wata ba sai ki daura dammarar yin aiki na fuskantar kalubalen da ke gabanki manya da kanana.

Misali:
akwai bukatar ki zamo mai nuna wa mai gida kulawa cikkakka,mai kara masa kwarin guiwa,mai taimakon sa bisa sauke nauyin da ke kan sa,mai rike asirin sa,kana mai mika masa yarda da aminci ki.

Akwai bukatar ki zamo mai yawan murmushi(hakika shi babban makami ne dake cin zukatan mazaje da yake),mai yin ba'a(wasa) da dariya,mai shagwaba,wani lokacin kuma ki zamo ke ce mai lallashi/rarrashi.

Akwai bukatar ki zamo mai nuna masa cewa da gaske fa kina SON shi(irin hudubar nan da ake wa mata cewa ba'a nunawa namiji soyayya ko sakin jiki dashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post