Dayawa cikin maza da matan wannan zamani bamu da masaniya Kan irin rawar da SHEDANUN ALJANU ke takawa wajan hanamu zaman lafiya a gidan aurenmu.

Dayawa cikin maza da matan wannan zamani bamu da masaniya Kan irin  rawar da SHEDANUN ALJANU ke takawa wajan hanamu zaman lafiya a gidan aurenmu. 

Abin zai baka mamaki yanda idan Har SHEDANUN ALJANU suka maida gidanka farfajiyarsu, kullum kaita ganin bacinrai Kenan. Wani sa'inma gani zakayi kanemi abinka ka rasa, kuma kasan daga Kai Sai ita a gidan. Sai kaga mutum Yana zargin matarsa, bayan Kuma aljanune suka sace. 

Abinda zai baka mamaki da tsoro Kan wannan lamarin shine, ganin yanda matanmu da samarinmu muka saki karatun Qur'ani da sauraronshi. Kafin kaga matar da take kunna Sheikh Abdulrahman Sudeas a gidanta, sai ka tona. Galibi gani suke Idanma bakya kunna SHEDANUN mawakan zamanin Nan, baki wayeba.  Bayan Kuma kunna karatun Qur'ani a gida shine yake korar SHEDANUN ALJANU. 

Tabbas idan Har munason tabbataccen zaman lafiya a gidan Mu. Sai mun Raya gidajenmu da sauraron karatun Qur'ani.

Post a Comment

Previous Post Next Post