GYARAN ZAMAN AURE*_➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖

_*GYARAN ZAMAN AURE*_
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖

_*✒ MATSALAR FARKO*_

 _*BAYA SHIGOWA GIDA DA WURI:* Yaya Yake Fita daga Gidanki? Idan ya fita Wane sako ki ke Aika Masa? Ya Kike Karbarsa Idan ya Dawo? Ya Yake Samunki? Ya Yanayin Gidanki Yake? Ya Makwancinsa Yake?_

_*✒ MATSALA TA BIYU*_

_*BAYA CIN ABINCINA:* Yaya tsaftar Wajen Girkin ki? Yaya Kike Shiga Kicin?  (Tsaftarki) Yaya Kike Hada Girkinki? Me Yafi so a Dafa Masa? Wadanne Irin kwanuka kike Amfani Dasu Wajen Zuba Abincinsa? Yaya Wajen da zai ci Abinci Yake? Ya Kike shirya Masa Kayan Abincinsa da zai ci? Ya Kike Karbarsa Lokacin da Yazo Cin Abincinsa?_

_*✒ MATSALA TA UKU:*– 
_*YANA DAURE FUSKA:* A Wane Hali ya Fita Daga Gidan?Yaya Yanayin Aikinsa Yake? Da Suwa Yake Harka Idan ya fita?Ya Yanayin Samunsa Yake?Idan ya Daure Fuska, Ke ya Kike Masa?_

_*✒ MATSALA TA HUDU:*– 

_*BAI DAMU DA NI BA:* Kin Sauke Masa Nauyin da *Allah* ya Dora Miki Nasa a Matsayin sa na Mijinki? Kina kula da Abin da Yake so Da Wanda ba ya so? Kina jin Damuwarsa a Ranki? Ya Kike Tafiyar Dashi? Ya kina Masa wasa ? Ya kina Nuna Masa kula da Mahaifansa da Danginsa ? Ya kina Masa Addu’ah ?_

_*MATSALA TA BIYAR*_

_*BAYA KULA DA YARA:* Yaya Tarbiyyar Yaran? Yaya tsaftarsu? Ya Suka Dauki Mahifinsu? Dawa Yaran Suke Harka?_

_*✒MATSALA TA SHIDA*_

_*YANA FITA YA BAR NI DA SASSAFE:* Wane Irin karba ya Samu da Daddare? Bayan Tashinsa Daga Bacci ya Kika karbe shi? Ya Yanayin Gidan yake?_

_*✒ MATSALA TA BAKWAI*_

_*IDAN NA YI BAQI YANA JIN HAUSHI:* Yayin da Kike da Bakin Wane Irin Kulawa Kike ba wa Mijinki? Kin Fifita Bakinki a kansa? Kina fifita ‘Yan Uwanki a kan Nasa? Wane Irin Baki kike yi?_

_*✒ MATSALA TA TAKWAS*_

_*BA YA YABA KWALLIYATA:* Wacce Irin Kwalliya Mijinki ya ke so? Yaya kike tsara kwalliyarki? Yaushe kike kwalliyar?_

_*✒ MATSALA TA TARA*_

_*BA YA HIRA DA NI:* Ya kike Hirar? Kin Iya Hirar ma Kuwa Wane lokaci kike Zuwa Hirar?_

_*✒ MATSALA TA GOMA*_

_*BAYA BARI NA FITA KOMAI_

 MUHIMMANCINTA:* Ya Kike fitar? Yaushe Kike fita da dawo wa? Kina sauke Nauyin Dake kanki kafin ki fita? Kin iya Tambayar fitar?_

_*✒ MATSALA TA SHA 'DAYA*_

_*YA CIKA FADA:* Me Yake sa shi fadan? Yaushe Yake fada? Akan Me Yake fadan? In yana fadan ya kike?_

_*✒ MATSALA TA SHA BIYU*_

_YANA KULA MATA A WAJE:* Son Yin Hirar dasu ne da shi? Ko Daukarsu yake su kebe? Me Yake so a jikin Mace? Shin kina Kyautata Masa Abinda Yake so a jikin mata? Ko a Hoto, Me kike ganin Yafi Sha’awa a Jikin Mace? Kina yi Masa hakan?_

_*✒ MATSALA TA SHA UKU*_

_*YAKI BARI NA IN SAKE DA MAKWABTANA:* Wadanne irin Makwabta kike da su? Yaya Mu’amalar Makwabtan na ki._

Idan kika gyara wayannan matsalolin to zaki dunga juya mijinki kamar waina

Ku danna bulun Rubutun dake kasa domin kasancewa tare da ku 👇👇👇

Malama Juwairiyya Bintu Outhman

Post a Comment

Previous Post Next Post