Amfanin da shan rake ya ke yi wa mace mai ciki, da wasu 9

Amfanin da shan rake ya ke yi wa mace mai ciki, da wasu 9 

Ga kadan daga amfanin da rake take yi a jikin mutum.
1. Rake na kara karfin kashi domin tana dauke da sinadarin ‘Carbohydrates’.

2. Rake na dauke da sinadarin ‘Vitamin A’ wanda ke kara karfin ido.

3. Shan rake na kare mutum daga kamuwa da zazzabi musamman idan aka matso ruwan aka sha.

4. Rake na hana lalacewan kumba,karyewa ko canza kala.

5. Rake na sa rauni ya warke da wuri.

6. Yana kuma taimakawa wajen samun kaifin kwakwalwa.

7.Shan ruwan rake na taimakawa wajen kawar da warin baki da lalacewar hakora

8. Shan rake na kwara da matsalar rashin haihuwa ga matan da ke fama da wannan matsalar, yana kuma bunkasa girman jinjiri a cikin uwar sa sannan yana hana mata masu ciki yin bari.

9. Rake na taimaka wajen hana jiki ya nuna tsufa da wuri.

Allah yasa mu anfana 👏

Post a Comment

Previous Post Next Post