*HUKUNCIN SUMBATA (KISS) DA RUNGUMA TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA*
*TAMBAYA:*
Assalamu alaikum Malam Watane tana Tambaya in sun hadu da saurayinta sai sunyi kissing suna hugging amma basa saduwa kuma tana so tadena wannan aikin amma takasa yazatayi Malam nagode
*AMSA:*
Wa Alaikumus salam, Dukkan godiya ta tabbata ga Allah.
Zina (yin fasikanci) ba wai yana nufin saduwa kawai ba, a'a, akwai zinar hannu, wato taba abinda yake haramun, da zinar idanu, wacce take ta kallon haram, duk da cewa zina wacce aka yi ta da al'aura, ita ce zina wadda ake azabtar da wanda suka yi ta da azabar haddi.
An karbo daga Abu Hurairata Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: *“Allah ya shar’anta wa kowane ɗan Adam rabonsa na zina, wanda ba makawa zai aikata. Zinar idanu ita ce kallo, zinar harshe itace magana, mutum yana iya buri da sha’awa, al’aura kuma ita ke tabbatar da haka ko kuma ta musanta”.* (Bukhari ya ruwaito shi, 5889; da Muslim, 2657).
Ba ya halatta ga musulmi ya yi kwadayin abubuwan da zasu kai shi ga zina, kamar sumba, kadaitaka, tabawa ko kallo, domin duk wadannan haramun ne kuma suna kai ga mafi girman sharrin zina.
Allaah ( تعالى ) yana cewa:
*وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا )*
Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya. (wato duk abin da ya ketare iyakokinsa: zunubi mai girma, kuma muguwar hanya ce wadda take kai mutum wuta face sai idan Allah Ya gafarta ma mutum). Suratul Isra’i 32].
Duban abin da yake haramun ne yana daga cikin kiban Shaidan, wanda ke kai mutum ga halaka, ko da bai yi da gangan ba tun farko. Allaah ( تعالى ) yana cewa:
*“Ka ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu (daga kallon haram), kuma su tsare farjojinsu (daga haram). Wancan ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne Allah, ga abin da suke aikatãwa Masani ne.*
*Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga ganinsu (daga kallon haram), kuma su tsare farjojinsu (daga haram)”.* [suratul Al-Nur 30-31]
Ka yi tunani a kan yadda Allah ya haɗa lamarin runtse ido da mas’alar kiyaye farji (kare farjinta) a cikin waɗannan ayoyi, da yadda aka fara ambaton runtse ido, kafin kare al’aura, domin ido yana rinjayar zuciya wajen aikata zunubi.
*Shaikh Abdul'Azeez bn Baaz (rahimahullah) yana cewa:* A cikin wadannan ayoyi guda biyu, Allah ya umurci muminai maza da mata da su runtse idanuwansu, su kiyaye farjinsu, saboda tsananin girman zina da abin da yake haifar da fasadi mai girma a tsakanin musulmi. Barin kallonsa ga abinda yake haram yana daga cikin abubuwan da ke haifar da cuta a cikin zuciya da faruwar ayyukan fasikanci, yayin da runtse ido yana daga cikin hanyoyin kiyaye kai daga hakan. Don haka Allah ( تعالى ) yake cewa:
*“Ka ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu (daga kallon haram), kuma su tsare farjojinsu (daga haram). Wancan ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa."* [Suratul Nur 30].
Runtse ido da kiyaye farjin shi ne mafi tsarki ga mumini duniya da Lahira, amma mutum ya bar kallonsa cikin walwala da rashin kiyaye farjinsa suna daga cikin manya-manyan sababi na halaka da azaba a duniya da kuma Lahira. Muna rokon Allah ya kara mana kare mu.
Allah ya gaya mana cewa shi Masani ne ga abin da mutane suke aikatawa, kuma babu wani abu da yake ɓoye a gare shi. Wannan gargadi ne ga muminai a lokacin da suke aikata abin da Allah ya haramta da nisantar abin da Allah Ya shar'anta musu, kuma tunatarwa ce a gare shi cewa Allah yana ganinsa, kuma ya san dukkan abin da yake aikatawa, na alheri ko waninsa. Kamar yadda Allah ( تعالى ) yake cewa:
*"ALLAH yana sanin ha'incin idanu, da abin da qirji ke boyewa".* [Surat Ghafir 19]
Ƙarshen magana Daga bakin al-Tabarruj wa Khataruhu.
Wajibi ne musulmi ya ji tsoron Ubangijinsa a boye da bayyane, kuma ya nisantar da abin da Allah Ya haramta na kadaita shi da wani ma'abocin jinsi, kamar kallo, ko musafaha, ko sumbata da sauran ayyuka na haram wadanda ke kai ga aikata fasikanci (zina).
Kada a yaudari juna da tunanin cewa ai ba zina ake ba, kawai dai sumbata ne da runguma, kuma shi wanda aka yaudara ya tsaya a kan wannan cewa ba komai bane, ko soyayya ce ko aure zamuyi, ya sani irin wannan laifin ke kai ga aikata babbar zina, kuma a karshe a zo ayi abinda za'a zo ana da - na - sani.
Kuma ayi duk iya kokari wajen nesanta kai daga wannan mummunar dabi'ar da kazantar, domin kazanta ce mace ta sa bakinta akan bakin saurayin da bata aura ba, bama ta gama sanin rayuwarsa ba, kuma zunubi ne mai girman gaske da ke kai mutum ga azabar Allah madaukaki.
Kuma babbar hanyar nesanta kai daga wannan mummunar dabi’un shine rabuwa da wanda ake yi dashi, da guje masa, da rashin haduwa dashi, da kuma tuba na gaskiya da istigfari, kuma mutum ya daure yayi aure sai ya huta daga irin wadannan kananan zunuban da sukan kai mutum zuwa shiga huta, Allah ya tsare mu. Akwai rubutun mu akan HANYOYIN GARKUWA DAGA ZINA in shaa Allah zasu taimaka wajen magance wannan dabi'a.
Wanda ya aikata daya daga cikin wadannan ayyukan to ya tuba ga Allah, domin duk wanda ya tuba Allah zai karbi tubarsa, wanda ya tuba kamar wanda bai yi zunubi ba ne.
Daya daga cikin mafi girman kaffarar irin wadannan zunubai shine yawaita salloli biyar akan lokaci. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Salloli biyar, da daga wata Juma’a zuwa wata, da kuma watan ramadan zuwa wani, suna kankare zunubban da suka shiga tsakani, matukar dai an nisanci manyan zunubai”. Muslim ne ya rawaito shi, 1/209
Kuma Allah ne Mafi sani.
*✍️Shashen Fatawowi Bisa Qur'ani da Sunnah, A Bisa Fahimtar Magabata Kwarai*