IDAN MUTUM YA SADU DA IYALINSA SANNAN YASO YASAKE KOMAWA SAI YAYI WANKA?:

IDAN MUTUM YA SADU DA IYALINSA SANNAN YASO YASAKE KOMAWA SAI YAYI WANKA?
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Idan Mace Ta Sadu Da Mijinta Sai Bayan Sungama Saiya Sake Neman Yasadu Da Ita, Shin Sai Sunyi Wanka Zasu Kara Saduwa Kokuwa?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
الحمد لله.
Sunnah ne ga namiji idan yasadu da iyalinsa sannan yai nufin sake saduwa da ita yayi alwala tsakanin saduwa biyun, amma dazai wanka shine yafi.

Daka Abu sa'idul khudri Allah yakara masa yarda yace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Idan ɗayanku yajewa iyalinsa sannan yaso yasake komawa yayi alwala tsakaninsu ) Muslim (466).

Awata ruwaya ta Ahmad ( Alwalar Sallah ) Arna-Uud ya inganta isnadin ruwayar yayinda yake ta'aliqin musnad Ahmad ( 3/28).
Shaiek Usaimeen rahimahullah yace: halaye ukune mutum kedasu anan.

1. Yayi wanka kafin yakoma wannan shine yafi kamala.

2. Inyaga dama yayi alwala kafin yakoma wannan baikai wanka kamala ba.

3. Yakoma batare da yayi wanka ko alwala ba, shine karshen daraja, amma ja'izine.

Abunda yakamata shine kada suyi bacci sai sunyi ɗaya cik

Post a Comment

Previous Post Next Post