RAYUWA DA MUTUWA

RAYUWA DA MUTUWA

"Sun tafi sun kwanta acikin kasa ba dan suna so ba, sai dan ajali yayi kira kuma kwana ya kare, anyi ciwo an sha wahala rayuwa tayi qunci daga karshe sun yi kwanciyar da babu tashi, haka kwanaki suke karewa akan mu, za muyi ta tafiya har zuwa ranar da za'a yi mana sallar da babu ruku'u balle sujuda, nayi zaton kwanaki zasu rike mun amana, nayi zaton shekaru za suyi yawa a kaina, sai naga sun kare mun a wannan rana.
.
Na yi burin abubuwa a rayuwa amma burin bai cika ba gashi ajali ya sauka a kai na, nayi burin na fadi wadansu maganganu ga masoya na amma numfashi yayi tsada ayau, yau nine cikin Makara na shigo a makare Ya rabbi ka yafe ni, da ace na san Mala'ikun mutuwa suna hanyar zuwa gare ni dana bayyana password dina ga yan uwa na, bayan sun dawo gida daga rufe ni su rufe Facebook dina, in sun rufe ni su rufe WhatsApp dina.
.
Sai dai rai yayi halin sa, makomar mu gun Allah, lallai naso ace kafin raina ya fice na nemi yafiyar wadanda na bata musu, sai dai mutuwa ta sanya min ankwa, da ace nasan wannan shine ramin da za'a sanya ni da na koma zuwa ga Allah tun kafin yau da aka komar dani zuwa ga Allah, lallai jiki yayi nauyi, kwanaki sun juya zuwa tunanin ranar haihuwa ta.
.
Yau ce ranar da zan kwanta kwanciyar da Umma ta baza ta iya tashi na ba, balle masoyiya ta, tashi na sai ranar tashin Shugaban halittu annabin da aka aiko zuwa gare ni (S.A.W), laifukan da nake yi nayi tunanin gyarawa da zuciya ta amma gabobi na sun ci amana ta, buri ya yaudare ni, nayi tunanin Zan samu shekaru masu yawa sai gashi ajali ya sauka a kaina.
.
Tunani nake yi, yaya cikin gidan mu zai kasance idan za'a fitar da gawa ta zuwa ga sallah? zan zamo abin labari, za'a rinka cewa a lokacin da wane yake raye kaza da kaza, amma fa ada nine nake labarin matattu, yau nine ake labari, naso na rike sallolin Nafila da farillai akan lokaci, rayuwa ta rude ni, yau nine ake wa sallah, nine ake tunawa, kafin sati guda nasan zasu daina tunawa dani.

Ya Allah!! Ka Gafarta Ma Iyayenmu,Malumammu,Sarakunmu,Diya da Jikokinmu,Kanisantar damu daga AzabarKA,Ka Gafarta Mana,Jikanmu da RahamarKA, Ka Kare Diyanmu daga Sharrin Zamani Kafin Mutuwarmu da bayan Mutuwarmu,Ka nisantar damu daga Sharrin Zamani. 

Ya Allah! Kabamu ikon taimakon addininKA,Kasa Muyi amfani da Rayuwarmu kafin Mutuwarmu,kuruciyarmu kafin tsufanmu,lafiyarmu kafin rashin lafiyarmu, 

Plow share My New Page 
👇👇👇👇

Zainab Sheikh Jafar Mahamud Adam

Post a Comment

Previous Post Next Post