MAHAIFIYA😢😢😢😢👉Yaron ya tambayi mahaifiyarshi :Miyasa kike kuka?

MAHAIFIYA😢😢😢😢

👉Yaron ya tambayi mahaifiyarshi :Miyasa kike kuka?

👉Tace: Saboda ni mace ce
sai yaron yace : Ban fahimta ba.
saita rungume shi  tace : Bazaka fahimta ba har abada.

👉Sai yaron ya tambayi mahaifinshi : Miyasa mama take kuka ba tare da dalili ba??
Sai yace : dukkan mata haka suke kuka babu dalili.
👉Har yaron ya girma ya zama babban mutum baisan dalilin kukan mace ba.

👉Sai yaron ya tambayi wani mai hikima : Miye dalilin kukan mata ba dalili ?

👉Sai Yace mai: Yayin da Allah ya halicci mace, sai ya bata kafadu masu karfi domin ta dauki nauyin duk duniyar nan, ya bata hannuwa masu taushi domin jaririnta yaji dadin reno, ya bata karfin halin da zata iya jure wahalar haihuwa, sannan da juriyar bijirewar 'ya'yan bayan sun girma.

👉Da karfin halin kula da iyalinta da damuwa dasu,  ya bata soyayyar yaranta mara yankewa koda suna cutar da ita.

👉DAGA KARSHE ya bata HAWAYE da zata zubar domin rage wahalar wannan nauyin. domin cigaban tafiyar rayuwarta.

👉Wannan shine raunin mace kwara daya :

Post a Comment

Previous Post Next Post