AMFANIN TAFARNUWA 🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
*🧄 TARI ASMA 🧄*
sai a jika garin tafarnuwa a hada da ruwa da zuwa baka, sai lokacin tarin a rinka sha, ko kuma a sha bayan kowace sa'a uku, yara masu tarin shika haka za'a yi musu, amma a hada musu da lemun Zaki bayan kowace sa'a , hudu sai a basu cokali biyu.
*🧄 KORE TSAKUWAR KODA 🧄*
a hada cokalin tafarnuwa da zaitun da makadunas , sai a rinka ci da safe.
*RADADIN CIWUKAN CIKI DA HANJI*
A sha tafarnuwa cikin madara bayan haka a ci kumasari cokali daya, za a sami lafiya da ikon Allah.
GUDAWA (ZAWAYI)
sai a ci tafarnuwa safe da yamma, a kuma sha ruwan da aka tafasa al-babunaj da shi.
KORE MAJINA DA TARI
A sa tafarnuwa cikin zuma baka da Rabin kofi na ruwan dumi, kullum da safe a sha, za a warke da ikon Allah.
*MAGANIN KARFIN MAZAKUTA DA MAN TAFARNUWA*
sai a shafe karkashin Zakari da kasan Mara bayan anyi tsarki.
CIWON HAKORA DA KUNNE DA MAN TAFARNUWA 🧄🧄
a shafawa hakoran, kunnen kuwa sai a dura da dare in za a kwanta , safe da yamma
amma kadan.
🧄 JINI MAI HAWA DA SAUKA 🧄
sai kullum bayan sallar isha'i a saka tafarnuwa cikin zuma, a yawaita sha, za a warke da ikon Allah.
🧄 KAZUWA 🧄
sai a rinka shafe jiki da man tafarnuwa kullum.
🧄 KUKAN KUNNE DA CIWUKANSA 🧄
sai a rinka dura man tafarnuwa safe da yamma.
🧄 KUMBURIN GABOBI DA CIWUKANSA 🧄
A HAda tafarnuwa cokali biyar, hulba babban cokali daya, khal babban cokali daya, zaitun kofi daya Wanda aka tafasa da gishiri Rabin cokali, bayan haka sai a hadasu guri daya, sai a boye shi, kullum da yamma a rinka shafe guraren ciwon da safe ma haka za a yi.
Allah zai ba da lafiya
🧄 KURAJE MASU WARI DA MIYAKU 🧄
sai a samo ruwan tafarnuwa kofi daya, zuma kofi daya , sai a hadasu guri daya, sai kullum da safe a shafa , sai kuma gobe da safe a wanke da ruwan dumi mai dan zuma da dan gishiri a ciki, sai a sake shafawa har a samu lafiya.
🧄 KURAJEN FUSKA 🧄
A samo tafarnuwa kofi biyu, zuma kofi biyu , sai a hada a rinka shafawa, bayan awa daya da shafawa sai a wanke da ruwan dumi.
🧄 SABODA MACIJIN CIKI 🧄
sai a dafa tafarnuwa cikin ruwa kamar minti 20 sai a karya da shi, ba za a ci abinci ba sai da azahar, haka za a yi sai bayan kwana uku.
🧄 TSAKUWAR KODA 🧄
a hada cokali daya cikin nono kindirmo, bayan nan sai a sha zaitun cokali daya, lemun tsami cokali daya kullum da safe kafin a karya.
🧄 FARFADIYA , HAUKA DA YAWAN WASU-WASI 🧄
a ci cokali daya na garin tafarnuwa da cokali daya na ruwan inabi (rabena) bayan kowane cin abinci .
sai kuma a rinka cin wadannan masu zuwa safe da yamma cokali cokali , kuma kowanne sai ka samo girma 50 , sai a hada sy guri daya cikin zuma kilo daya, sai kuma a yawaita sha zamzam..
¹ ya'yan baushe
² tsamiya
³ barkono
⁴ aduwa. Allah zai warkar da shi insha Allah.
🧄 MAGANCE TARIN HUKA 🧄
sai a dafa tafarnuwa a rinka shakar tururin, sai kuma a sha madara da tafarnuwa a ciki, sai kuma a sha zuma Rabin kofi, musamman a rinka sha da safe.
🧄 CANCER TA JINI KO TA NONO 🧄
sai a samo zuma kilo 2 da kakinsa, hancin abarba giram 250, garin tafarnuwa giram 250 , garin habbatussauda giram 500 da kuma giram 50 na filasko sai a hada su guri daya a rinka sha to kowane nau'in (KANSA) NE ALLAH ZAI WARKAR DA SHI .
🧄 SIKILA/LAULAYI , YAWAN CUTA 🧄
a samo tafarnuwa cokali daya kwai uku ko abinda ya samu, da dan gishiri da al-kammun cokali daya, sai a soya da man zaitun, kullum a rika haka har jiki ya warware, kuma ba dadewa za a samu lafiya da yardar Allah .
alhamdullah
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄