Halaye ( 12 )dake hana ma'aurata jin dadin zama a aure :-

Halaye ( 12 )dake hana ma'aurata jin dadin zama a aure :- 

1. kayi kuskure a faɗama amma ka ƙi yarda da kuskure balle har ka/ki gyara 

2. Ka san kayi laifi amma a ƙi bada hakuri sai dai ƙa bada dalili da hujjojin da yasa ka yin wannan laifin ( justifying laifi) 

3. Yawan Fushi :-  komi qanqantan abu anyi fushi, ka ƙi lallabuwa, ayi ta jan aji, basarwa, kyaliya, magana ciki ciki, a kubura kumatu da ayita hura hanci wai a dole ana fushi an tsare gida. 

4. Riqo ayi :- daga an samu saɓani baza'a zauna a magance matsalar ba, sai ayi ta gaba, ayi ayi a shirya amma sai riqo, ko abu mutum yayi sai an tuna mar da laifin da akayi masa, aki yafewa koda an nuna nadama an bada hakuri amma duk da haka aki sakewa a koma normal.

5. Ramako ( revenge) duk abunda daya yayi na ba dai dai ba sai an samu hanyar da an raba, a zauna kusan kullum ana saƙa da nemon hanyoyin da za'a rama abunda daya yama daya. Kullum ana cikin " bazan yafeba sai na rama abun da aka min " sai na nuna masa/ta matsayinta" "sai ta/ya gane kuskurenta/sa" etc. 

6. Watsi da kyawawan halaye da dabi'un juna da sa hankali akan munanan halayen juna da nuna gazawar juna. 

7. Rashin godiya da yabawa, a kyautatama amma ka banzatar da abun tamkar bakomi akayima ba, ba nuna farin ciki, jin dadi balle a yaba balle ayi godiya. 

8. Mai da abokin zama tamkar marar hankali ko karamin yaro ko yarinya, da sunyi magana a nuna gazawar hankali, tunani, qarfi, arziki etc. 

9. Barin negative energy a tsakanin kullum fiye da positive energy kullum cikin faɗa, damuwa da kunci, ba nuna farin ciki, jin daɗi da walwala, kullum mutum yana da abunda ke damun sa

10. Mai da laifi akan marar laifi, ko daukan damuwa ka daurama wadda baida alaqa da ita. 

11. Son kai da son zuciya duk abunda ba zai yi amfane ka ba bakayi, ko duk abunda in dai zai amfane ka baka damuwa da wadda zaka cutar dan samun abunda kake so. 

12. Rowa yakan hana aji dadin zama da mai hali irin haka mace ko namiji. 

✍️ Fatimah Chikaire

Post a Comment

Previous Post Next Post