Ko ka san amfanin gawayi a gida kuwa?
Gawayi na daya daga cikin abubuwan da mutane ke dauka abin banza a gida. Ana dauka da muhimmaci ne kawai lokacin da bukatarsa ta taso. Amma kuma, matukar kana neman taimako na farko (first aid) gawayi abu ne da ya kamata ka bukata a kowane lokaci. Ba za ka fahinci wannan ba, amma dai dai yana daga cikin magunguna da ya kamata ka tanadar a gida saboda gudummawa da yake bayarwa.Dubi: Amfanin na'a-na'a a jikin dan adam
Wata kila, ba ka ba shi daraja ko muhimmanci. To lokaci ya yi da ka dauke shi da muhimmanci. Ga jejin amfanin gawayi guda goma sha uku da ba ka tsammani kamar haka:
Yana cire wari:
Idan takalmanka suna wari; samu gawayi ka sanya ciki, ko kuma idan daki ne sai ka nemi wurin da yake warin ka jefa gawayi kawai zai daina, ko kuma idan firinji (fridge) ne cikin ke wari kawai jefa gawayi ciki zai daina. Saboda haka gawayi na dauke wari kowane iri ne in ya dame ka
Yana kashe gubar dake cikin abinci (kayan lambu)
Al’umma kan koka kan yadda ake amfani da takin zamani ga abincin da muke nomawa musammam kayan lambu wanda sakamakon sa takin kan kasance kamar da guba a cikinsu. To kawai in ka samu irin wannan kayan lambun sanya gawayi ciki ka barshi zuwa safiya.
Yana taimaka wa abinci mai rubewa (kayan lambu) ya jima bai lalace ba.
Yana washe hakora su yi haske:
Idan kana son hakorinka ya yi haske, kar ka bata lokacinka wajen sauraron abin da masu tallan kayan wanke hokori su ke cewa, kawai samu gawayinka ka nika ya yi laushi. Sai ka sami hancin plantain (ayaba) ka rika tsomawa kana goge hakoran na tsawon mako guda.
Yana sake gyaran miyar da ta dauki lalacewa
Idan miya ta dauki lalacewa in ta kwana da safiya kawai kar ka zubar nemi gawayi ga jefa cikin miyar a dora kan wuta a dumama zai dawo da darajar miyar kamar da.
Yana rage karfin abin sha mai alamar bugarwa
Duk abin sha mai dauke da gas idan ya kwana, in kana shakkar sha don wani abu da ka ji. Kawai tauna gawayi ka sa a ciki ka sha, an wuce wurin kenan.
Yana cire tsami a cikin kunun zaki:
Idan baka son kunun zakin da aka dama ya yi tsami kamar giya, ta zarar an dama kunun sai a nemi gawayi a jefa ciki ya kwana zuwa safiya, lafiya lau ne.
Yana washe fiska da kuraje suka bata
Kawai nika gawayi ka shafa a wurin
Yana busar da gyambo mai mugunya in aka nika aka sa garin a ciki
Yana taimakawa wajen kwartar da dattin cikin ruwa in aka jefa su ciki
Idan cikin ka ya kumbura shafa gawayi a kai zai sace cikin lokaci kalilan.
Yana cire dattin da ya kama jikin tiles a bayan gida ko dakin girki (kichen).
Yana kuma maganin gyambon ciki (Ulcer) kasance mai taunawa akai-akai zai taimaka matuka.
Mai karatu na iya dubamakalunmu na baya damuka wallafaakan kiwon lafiya damakamantansu. Dubi misalin makalar kamar haka: Amfanin kanwa a jikin dan adam