Bismillahi wassalatu wassalamu ala rasulullah, khusbara yana dauke da sinadarai masu matukar mahimmanci ga lafiyar dan adam don haka wasu kasashe irinsu india suka maidashi abincinsu na yau da kullum .
KADAN DAGA CIKIN AMFANINSA.
* Yana magance dukannin cutar da ta shafi fata irinsu tau-tau,kefsi,kanzuwa,pimples,kaikaiyin jiki da sauransu.
YADDA AKE AMFANI DASHI :Sai asamu garin khusbara kwaba da zuma ashafe jiki dashi bayan minti 15 sai a wanke haka za'a rinkayi har tsawon sati guda.
*Yana magance kurajen baki idan aka tafasashi ana kuskura baki dashi safe da yamma.
*Yana kara yawan gashi da tsawo dasakashi baki idan aka hada garinsa da man gashi ana shafara agashi sau biyu duk sati.
*Yana narkar da abinci kuma yana bude kafofin jin idan aka jikashi ana shansa kullun da safe kafin a karya.
* Yana manganin sanyin jiki da mura idan ana barbadawa a abinci mai dumi.
*Yana ciwon suga (diabities) idan na kijikashi da ruwa litre daya ashanye ayini daya ana fara shansa kafin a karya haka bayan an karya har litre dayan ya kare.
*Yana kashe kwayoyin cuta kowani iri (bacteria) sai ayi yajin garinsa ko kuma ahada garinsa da curry arinka cinsa a abinci ko sallad.
*Domin cutukan da suka shafi ido ko yanar ido sai ajika khusbara arinka wanke ido dashi safe idan an tashi daga bacci da dare kafin a kwanta bacci.
*Domin magance ciwon ciki ko mara na mata a lokacin Al'ada sai asamu cokali biyu na garin kusbara da sugar(sukari) cokali daya sai a tafasa da ruwa litre daya ya tafasa sosai sai asha da dumi duminsa wallahu ta'ala a'alam.