Amfanin “dauΙ—ar kunne” da illar Ζ™waΖ™wale ta:πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½

Amfanin “dauΙ—ar kunne” da illar Ζ™waΖ™wale ta:

πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½

“DauΙ—ar kunne” wani ruwa ne mai Ι—an danko da dodon kunne ke samarwa domin bai wa kunne kariya, saΙ“anin yadda Bahaushe ke cewa “dauΙ—ar kunne” ce . Saboda haka “dauΙ—ar kunne” ba dauΙ—ar kazanta ba ce, face wata hanya ce da kunne ke samar wa kansa kariya daga baΖ™in abubuwa da ka iya shigowa daga waje.

Allah da ikonsa, kamar yadda kunne ne ke samar da wannan “dauΙ—ar kunne”, haka nan kunnen ke da ikon yashe wannan “dauΙ—a” da kansa.

Daga cikin amfanin “dauΙ—ar kunne” akwai:

Cafke dukkan nau’in Ζ™ura, Ζ™asa, Ζ™wari ko yayi kafin su kai ga cikin kunne.

Kashe kwayoyin bakteriya, da sauransu.

Saboda haka kada ka yi amfani da waΙ—annan abubuwa don Ζ™waΖ™wale dauΙ—ar kunne:

Magogin kunne wato ‘cotton bud’ a turance.

πŸ‘‚πŸ½ Tsinken tsintsiya
πŸ–Œ️ Mirfin biro
✒️ Kan ashana
πŸ‚ Gashin kaza, da makamantansu.

Sanya waΙ—annan abubuwa cikin kunne don Ζ™waΖ™walo “dauΙ—ar kunne” na da haΙ—arin:

Ƙara cusa “dauΙ—ar” zuwa can cikin kunne.

Kareraya gasun cikin kwararon kunne, wanda suke amfani wajen kare kunne daga baΖ™in abubuwa daga waje.

Cusa irin waΙ—annan abubuwa na da haΙ—arin shigar da Ζ™wayoyin cuta cikin kunne.

Raunata gangan kunne yayin da irin waΙ—annan abubuwa suka zarme cikin kunne.
Shafe ko manne “dauΙ—ar kunnen” a kwararon kunne.

Haka nan, zira waΙ—annan abubuwa cikin kunne don susa ko Ζ™waΖ™walo “dauΙ—ar” akai-akai zai share kwararon kunne, kuma share Ζ™wararon kunnen na nufin share kariyar da Allah ya shirya wa kunne. Saboda haka, dukkan baΖ™in abubuwa na iya kutsa kai cikin kunne kai tsaye.

Kada ka Ι—auki Ι—abi’ar sa magogin kunne cikin kunne don goge “dauΙ—ar kunne” kullum.

TuntuΙ“i likitan kunne da zarar ka fara jin wani Ι“aΖ™on yanayi a kunnenka, ko neman shawarwari kan tsabtace kunne daga “dauΙ—ar kunnen”.

Post a Comment

Previous Post Next Post