MAGANIN NANKARWAAssalamu'alaikum Dan Allah ka taimaka min da maganin nankarwa stretch marks Nagode sosai Allah Ya Kara basira Ameen

MAGANIN NANKARWA

Assalamu'alaikum  Dan Allah ka taimaka min da maganin nankarwa stretch marks Nagode sosai Allah Ya Kara basira Ameen

Da farko dai shi Nankarwa wasu tabbai ne layilayi da suke fitowa mace a jiki musamman wacce ke dauke da ciki zuwa haihuwa Wanda idan anyi maganin sa da wuri wato daga fitowar sa zasu iya bacewa gaba daya amma barin shi ya dade kan hana sa bacewa gaba daye sai dai zai dushe ya zama dan kadan kadan ake iya gani

Suna fitowa ne a wurare kamar haka :-

Cikin mace daga kasa (mara)
Cinya 
Saman mama 
Mazauni 
Saman hannu ta wuraren hammata 
Da sauran su.

ME KE KAWO NANKARWA ?

Akwai abubuwa da dama da suke sa nankarwa kamar:-

1- Daukan ciki zuwa haihuwa (wannan shine babban abinda ke kawo nankarwa)

2- Ramewa tashi daya (ga mutum mai qiba)

3- Yin qiba tashi guda (ga mutum mai rana)

4- Gado daga mahaifiya
 
5- Jinya na tsawon lokaci
 
6- Damuwa mai yawa da makamantar su

MATAKAN NANKARWA 
Yana da matakai guda uku gasunan kamar haka:-

1) Farko fitowar sa zaki gansu sirara yana da pink kala sannan yakan yi kaikayi wannan matakin bashi da wahalar magani

2) Zai zama ja ko ruwan bula sannan girman su zai karu yanzun kam babu kaikayi sai lokaci zuwa lokaci zai iya bacewa ki ya ragu ya danganta da yanayin jikin mutum

3) Zai zama fari ko ruwan silva wannan kam yana da matukar wahalan magani sai an jure shims din sai dai ya ragu ba wai ya bace baki daya ba.

HANYOYIN MAGANCE NANKARWA

Ruwa
Ruwa da Kuke gani yafi komai mahimmanci a jikin dan Adam. Rashin shan ruwa yana sa jikin mutum ya bushe ya tattare tare da saurin tsufa a yayin da yawan shan ruwa kofi 8-10 kullum yake sanya taushin jiki da kyawun fata kuma da hana wasu cututtuka da dama kama fatar mutum da wuri.

MISALIN YANDA ZAKA SHA KOFI 8 ZUWA GOMA ACIKIN KO WACCE RANA

-Kofi 2 da zaran kin gama wanke baki da safe.

-Kofi daya bayan karin kumallo.

-kofi Daya Kafin azahar kisha.

-kofi Daya kafin abincin rana daya bayan kin gama ci.

-kofi daya da la'asar.

-kofi Daya kafin abincin dare kofidaya bayan kin gama ci.

Allah yasa mu dace
Kabir Yusuf Danwurin Dutsi
Da fatan kowa ya Tashi lfy

Post a Comment

Previous Post Next Post