MAGUNGUNA 17 DA AKE YI DA MAN DIYAN DARBEJIYA.Zamu takaita kamar haka

MAGUNGUNA 17 DA AKE YI DA MAN DIYAN DARBEJIYA.

Zamu takaita kamar haka :

Man diyan darbejiya mai ne da ake samu kai tsaye daga 'ya'yan darbejiya.Kimiya ta zayyano cewa akwai wasu sinadarai masu karfin gaske dake kashe kwayoyin cuta na bacteria da fungi(anti bacteria and anti fugal infection) a cikin su.

Man diyan darbejiya yana da daci (bitter taste) a sanadin samuwar sinadirran phytochomicals da titerpenoid.Gangariyar man diyan darbejiya na kumshe da fatty acid da alkanoids.

Man diyan darbejiya na ainihin baya da wani lahani (non toxic in nature) ga halittu yala ga mutane ko dabbobi.A wasu lokuttan dabbobi kan ci darbejiya musamman idan suna fama da wasu cutukkan da suka shafi ciki ko masu lailayi a cikin baki.

1.Man darbejiya na warkarda kusan kashi 70 na cutukkan fata kamar su

Makero

Kazwa

Cin ruwa

Garjen giwa

Kaikayin fata

kuraje a sanadin cizon wasu kwari

2. man darbejiya na lausasa fatar data bushe.Mai neman fatar jikinsa tayi laushe ya jarraba ya gani.zai yi mamaki.

3. Man darbejiya na warkarda kunan rana dake 6ata fuska inda zaka ga mutum fari da shi amma fuskarsa baka.ko yana baki amma fuskar tashi tafi fatar jikinsa dushewa.

4. Man darbejiya na warkarda kuraje masu kaikayi a kan fata da ake ta'allakawa da fungal infection.

5. Man darbejiya na kare fatar jiki daga kwayoyin cuta na bacteria.

6. Man darbejiya na maganin kefsi

7. man darbejiya na maganin pimples da suka mamaye fuskar mace ko namiji.

7. Mai ne da yafi kowane mai inganci musamman ta 6angaren gyaran gashi domin yana rina gashi yana kashe kwayoyin cuta dake lailayi a cikin kai musamman ga mata masu jin kaikayi ko wasu kuraje dake tsira a cikin fatar kai masu kaikayi ko zafi.

8. Man darbejiya yana warkarda tsagewar fatar jiki da bushewarta da garjin fata dama duhun fata.

9. Man darbejiya na maganin cutukkan baki(mouth infections) kamar wanda ke brush yana ganin jini a hakoransa ko wanda dasashin sa ke kumbura yana masa ciwo.

10. Man diyan darbejiya yana maganin keyar kai musamman ga mata.
Sai a banye kai a saka toka a wanke da ruwan dumi a nemi man darbejiya original a shafa a shace da kyau washe gari za a ga yanda keyar zata mutu.

11. Man diyan darbejiya na maganin kunar fata a sanadin wuta.

12. Man diyan darbejiya na maganin dandruff ga maza da mata.

13. Man diyan darbejiya na maganin kurajen nan da ake kira chicken pox.

14. Man diyan darbejiya na maganin cutukkan ciki sai a nemi mai kyau a zanka shan 5ml a kullum za a ji banbanci a jiki.

15. Man diyan darbejiya na maganin kaikayin matse matsi a sabili da herpes.

16. Yana maganin ciwon daji kamar na mamma breast cancer da skin cancer waton cutar daji ta fata.

17. Masu hada maganin kwari na amfani da man darbejiya da masu hada maganin cutukkan ciki da kuma mafi yawan maganin cutukan fata na shafawa cream da ointment  na daukeda man diyan darbejiya,a sabili da dimbin tasirinsa a faujin maganin mafi yawan cutukkan fata.

Idan za a nemi man diyan darbejiya to a nemi original yana da launin dorowa da kuma kamshi kamar na tafarnuwa.
Akwaivmade in Mumbai India,  Indonosia da kuma Made in Egypt.Duka suna da kyau.

Dan Allah a ayi share

Post a Comment

Previous Post Next Post