Aslm AlykumDr inada tambaya ko Neman Shawara,'Yayan Gailona, Daya Daga ciki idan nataba sai inji wani Abu kololo karami iyakarsa Girman Kashin awaki makale ga Dan gwailona Daya, shine nace ko Akwai wata matsala ne ?

Aslm Alykum
Dr inada tambaya ko Neman Shawara,

'Yayan Gailona, Daya Daga ciki idan nataba sai inji wani Abu kololo karami  iyakarsa Girman Kashin awaki makale ga Dan gwailona Daya, shine nace ko  Akwai wata matsala ne ?

Kullutun da kake ji a cikin dan-marainanka zai iya zamowa daya daga cikin abubuwan ne:

1. Kullutu mai gundar ruwa (cyst).

2. Kullutu mai fitowa a jikin halittar dake samarda maniyyi (epididymis cyst).

3. Kumburin jijiyoyin jini a cikin marainan (varicocele).

4. Taruwar ruwa a cikin fan-maraina (hydrocele).

5. Karin cutar cancer a cikin dan-maraina (testicular tumour).

Don haka ya kamata kaje asibiti domin ayi bincike a tabbatar da abinda yake faruwa dakai.

Post a Comment

Previous Post Next Post