SHIN KO KUN SAN.● Zuciya tana daya daga cikin gabobin jikin dan adam masu matukar muhimmanci.

SHIN KO KUN SAN.

● Zuciya tana daya daga cikin gabobin jikin dan adam masu matukar muhimmanci.

● Zuciya tana nan a cikin ƙirji kuma tana samun kariya sosai daga kasusuwan hakarkari. 

● Zuciya tana da nauyi tsakanin 250g zuwa 350g.

● Zuciya tana fara bugawa bayan sati hudu da daukar ciki, sannan ba ta dainawa har sai bayan mutuwa.

●  Zuciya tana bugawa kusan sau 100,000 a kowacce rana.

● Zuciyar mutum babba tana bugawa kusan sau 60 zuwa 80 a minti daya.

● Zuciyoyin jarirai suna bugawa da sauri fiye da zuciyoyin manya da kusan bugu 70 zuwa190 a minti daya.

● Zuciyar mace tana matsakaicin karin bugu takwas fiye da zuciyar namiji a cikin minti daya.

● Sautin bugun zuciya yana faruwa ne sakamakon rufewar heart valves.

⚫ Zuciya tana bayar da jini ga duka sassan na jiki illa banda kuryar ido (cornea of eye), wanda shine saman ido na waje.

● Hanyoyin jini a jikin babban mutum sun kai kusan kilomita 100,000 gabaɗayan su.

● Wasu hanyoyin jini suna da kankanta sau ninki goma fiye da gashin mutum.

⚫ Mafiyawancin manyan mutane sana da kusan lita biyar na jini mai zagaya a jikin su.

● Saboda kasancewar zuciya tana da nata electrical impulse, za ta iya ci gaba da bugawa koda an rabata da gangar jiki, matukar tana samun isasshiyar iskar oxygen.

فَتَبَارَكَ اللَّهُ أَحْسَنُ الْخَالِقِينَ

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

Previous Post Next Post