BINCIKEN WAYAR MIJI...

BINCIKEN WAYAR MIJI...

Yana ɗaya daga cikin mummunar ta'ada da mata suka riƙe a wannan zamanin ta hanyar bincike a wayoyin mazajen su da niyyar gano ko suna soyayya da wasu, ko kuma dai suna ɓoye musu wasu abubuwa da suke yi a ɓoye, wasu matan suna so dole sai sun san sirrin yadda MAZAJEN su suke gudanar da sana'ar su, ma'ana nawa suke samu?? ko  a wajen aikin su..

Idan har mace ta fara saka zargi a ran ta, to tabbas Aure zai fara samun gargada..
Mafi yawancin mata masu zargi daga zarar sun gano abin da suke tsammanin sai ya zamo an tayar da babban yaƙi a gidan da hakan ka iya jawo mutuwar aure..

Mata ku kawar da kai daga zargi da tuhumar wayar mazajenku..

Ku kuma maza ku ji tsoron Allah ku kiyaye aikata wani abu mara kyau.
A ɗaya ɓangaren ana samun Wasu ma'aurata da sun yarda da junansu har ma suna iya daukan wayoyin  junansu suyi amfani dashi..

A ƙarshe dai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki, kuma ƙazantar da ba ki 
gani  ba tsafta ce.

Kuma ko da a ce mijin ki ba ya yarda ki ɗauki wayar shi babu laifi idan shi 
ya ɗauki taki, domin shi addini ya ba shi dama  ya ƙaro wata ta zama 
kishiyar ki...

Allah ya ba kowa zaman kafiya a gidajensa Na aure

Post a Comment

Previous Post Next Post